BOYAYYEN ALAMARI complet

BOYAYYEN ALAMARI complet
Saturday, 2 February 2019

€€€€€€€
BOYAYYEN AL'AMARI

Na Seema
Complet ebook
Ebook creat by Shuraih 99%
Publish by hausa Ebooks
.
Assalam shafin hausaebooks na gaisheku ayau muna dauke maku da littafin BOYAYYEN AL'AMARI na jajirtaccciya marubuciya Seema littafin ya kayatar gamida fadakarwa
.
Kadan daga ciki
Aleeza tsayawa tayi tana kallon shi ' shima d'in kallonta yakeyi yana smiling, Hakan yasa tayi sauri ta d'auke kanta tare da cewa.
"Bani phone d'inka inkira Yaya na!."
Khalil ciro wayar shi yayi k'arar IPhone8 ya mik'a mata gamida cewa.
"Meyasa bazaki kira Mum ba?."
"A'a, Banason hankalinta ya tashi ne."
Murmushi yayi tare da girgiza kai yace.
"Ita ya dace ki kira not your brother."
Aleeza ba tare da taimashi gardama ba tayi dialing number d'in Hajiya, Cikin sa'a kuwa ringing d'aya tayi ta d'auka, Aleeza tayi gyarar murya tace.
"Hello Hajiya!."
"Na'am Aleeza ' wannan number d'in waye."
Aleeza kallon Khalil tayi tace.
"Meye sunan wajen nan?."
"Private Hospital Girmi."
Nan ta maida wayar a kunnenta tace.
"Hajiya ina private Hospital Girmi, Kuzo."
"What! Subhanallah ' meyafaru dake Auta?."
Umma ta fad'i haka tare da mik'ewa tsaye.
"Hajiya please ki kwantar da hankalinki ' accident ne but banwani ji ciwo ba."
"Shikenan gamu nan zuwa da yayanki."
Abunda Hajiya tace kenan ' ta shiga kiran Hafiz, Bayan ya fito tsakar parlor ne Hajiya ta sanar dashi komai, Hakan yasa shi matsawa kusa da ita ya zaunar da ita sannan yace.
"Hajiya ki kwantar da hankalin ki, Ki sanya hijab ' ni bara inje intada mota."
Hajiya sawa tayi 'yar aiki ta d'auko mata hijab, Sannan shi kuma Hafiz ya fita harabar garage ya umurci gate man ya bud'e masa gate.
Bayan shigarsa mota ne Hajiya ta fito ta shiga motar suka wuce.
B'angaren Aleeza kuwa tunda ta gama wayar ' taketa juya wayar a hannunta, Shi kuwa Khalil smiling kawai yake sakar mata.
"Tai maki kyau ne?."
Taji tambayar kamar daga sama, Hakan yasa ta juyo ta kalleshi ' sannan ta maida kallonta kan wayar tare da mik'a mashi.
"Idan kinaso ' to nabaki halak malak."
Had'e rai tayi ta wurga mashi wayar shi tace.
"Cemaka akayi banda waya? Kokuwa fad'a maka akayi inada buk'atar wayarka?."
"Allah ya baki hak'uri! Amma meyasa kike yawan tunani?."
"Bangane ba."
"Yes dear, Kina cikin damuwa ko! Hakan yasa kikasha maganin da yafi k'arfin jinin ki which is very bad, Karki sake shan magani irin haka kinji ko?."
Kai ta d'aga mashi cike da shagwab'a idanuwanta duk sun cicciko da hawaye.

.
Domin karanta cikakken littafin sai ku download na shi a nan
.
Domin dauko PDF sai ku danna bulue din rubutun nan
DOWnLoad PDF formats
.
Domin dauko TXT sai ku danna blue din rubutunnan
DOWnLoad TXT formats
.

Domin dauko DOC kuwa sai ku danna blue din rubutunnan na kasa
DOWnLoad DOC formats
.
Kada dai ku manta littafin kala ukune akwai PDF,TXT da DOC
Sai ku zabi wanda zai iya budewa a wayoyinku,
.
Masu wayoyin Android da computer ina baku shawarar ku dauki PDF,
.
Masu kananun waya, ku dau TXT shine ke budewa a karamar waya duk kankantar ta kuwa
.
Domin karin bayani akan PDF,TXT da DOC sai ku shiga nan www.hausaebooks.com.ng/about
.
Ga duk mai son ya turo mana da littafainsa mu sanya a wepsite na mu sai ya turo ta adireshin Email dinnan
HAUSAEBOOKS@GMAIL.COM
.
Domin bamu shawara ko jinjina ma aikinmu duka ku tuntubemu ta Email namu hausaebooks@gmail.com
.
Domin wani bukatan na daban sai ku tuntubi Shuraih Usman mamallakin wannan shafi na Hausaebooks.com.ng ta hanyar danna nan www.fb.com/shuraih.usman
@www.hausaebooks.com.ng
@www.fb.com/hausaebooks
Release date:- 02/02/2019

0 Response to "BOYAYYEN ALAMARI complet"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel