TSATSUBA littafi na daya 1
Sunday, 12 August 2018

TSATSUBA
Littafi na daya 1
Hausa ebooks
Abdulaziz Sani m Gini
Made by Shuraih Usman
Typing:- Al'amin Ahmed Misau
•••••••••••••••••••••••••••••••••
Kadan daga ciki
SARAUNIYA LARBISA TA KASANCE GAGARUMAR ATTAJIRA kuma gagarumar mayakiya mai mulkin wata kasa
babba wacce tafi dukkan sauran kasashen duniya
girma da yawan jama ah a zamaninta
sarauniya larbisa ta tara zakakuran mayaka
wadanda suka kasance GUGUWAR ANNOBA domin duk kasar da suka durfafa
da yaki sai sun murkusheta komai karfin mayakanta
babbar matsalar sarauniya larbisa itace
bata tsafi kuma tsafi baya cinta bokaye sun
tabbatar mata da cewa ba zata taba haihuwa ba
sai ta lalata dukkan tsafin dake duniya gaba daya
idan kuwa tana son ta lalata dukkan tsafin duniyar dolene ta tura a nemo
mata wani littafi mai suna TSATSUBA
wanda aka rubutash sama da shekaru dubu arbaIn da suka gabata
A salin wannan littafin mallakin sarkin bokayan
Aljanu ne na farko wanda shine ya kirkiro
dalasiman tsafi guda miliyan dubu Arba'in daya
rubucesu tsaf a cikin wannan littafi kuma yayiwa
littafin lakabi da suna TSATSUBA
Duk wani tsafi na duniya mafarinsa kenan kuma
makarinsa na cikin wannan dalasimai tsawan shekaru dubu Arba in din da
suka gabata bokayen duniya da yawansu
suka bazama neman wannan littafi har suka hallaka bisa wannan tafarki
kuma duk wanda ya tsananta nemansa hallaka sukeyi
saboda tsananin tsaron da aka yiwa littafin
lokacin da sarauniya sarauniya larbisa taji wannan
batu na littafin TSATSUBA sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abinda ke mata dadi a duniya
bayan tayi dogon tunani da nazari saita watsa shela a ko ina a cikin duniya cewa duk
wanda ya samo mata wannan littafin na TSATSUBA shi zata aura kuma zata raba
kasarta da dukiyarta ta bashi kaso daya
shidai wannan littafi na TSATSUBA duk wanda ya
mallakeshi sai ya mulki komai da kowa na duniya
hatta dabbobi da tsuntsaye kuwa domin
zasu rinka bin duk umarnin da ya basu bisa wannan
dalili ne matsafa da sarakai da manyan jarumai
suka bazama neman littafin TSATSUBA suka rinka mutuwa a kokarin neman nasa.
Abin tambaya a nan shine waye zai iya baiwa
sarauniya larbisa littafin TSATSUBA alhalin yasan
cewa idan yana tare da littafin ita kanta zai iya
mallakarta kuma zai sami kowace irin dukiya da yake so ko matsayi
?
Masana da matsafa sun tabbatar da cewa babu
wata mai kyan fuska da kyan jiki tamkar gimbiya
larbisa a zamaninta kuma a wannan lokaci
data bayar da shelar a nemo mata littafin
TSATSUBA shekaranta ashirin daidai A duniya
kuma tun tana da shekara goma sha biyu ta hau kan karagar mulki sarauniya larbisa
bata da wani buri wanda yafi ta sami magajinta kafin
tsufa ya risketa don kada mulkinta ya tafi hannun
wanda ba jininta ba kasancewar itace kadai ta rage
a irin zuri ar gidansu
•••••••••••••••••••••••••••••••••
Shin sarauniya larbisa zata samu nasarar mallakar littafin Tsatsuba kuwa
Amsar yana cikin littafin
.
Sai kuyi marmaza ku sauke littafin zuwa kan wayoyinku, anan kasa
.
DOWNLOAD AS PDF EBOOK
DOWNLOAD AS DOC EBOOK
DOWNLOAD AS TXT EBOOK
Kar dai ku manta littafin kala Uku ne akwai TXT,PDF da DOC sai ku zabi wanda zai iya budewa a cikin wayoyinku batare da wata mishkila ba
.
Daga taskar hausaebooks
www.shuraih.waphall.com
0 Response to "TSATSUBA littafi na daya 1"
Post a Comment