TSOHON ALKAWARI complet na NaZir Adam Salih
Sunday, 12 August 2018

Hausa ebooks
TSOHON ALKAWARI
Nazir Adam Salih (m)
Made:- Shuraih Usman
•••••••••••••••••••••••••••••••••
Lallai wannan littafi yaci sunansa na TSOHON ALKAWARI, tabbas Nazir Adam Salih ba karamin fasihin Marubuci bane don kuwa dole na koda shi, sannan na yabeshi, saboda irin salon rubutunsa
.
Baya taba rubutu mara ma'ana , sannan dukkan littatafansa akwai darussa sosai acikinsu, amma mai hankaline kadai zai gane hakan
.
Nazir Adam Salih yana daya daga cikin marubutan hausa wayanda littatafansu yafi tashe a kafafen sadarwa,
Kai ni zan iya ce maku in ka dauke Abdulaziz Sani madakin gini, toh babu wanda akafi yawan post na littatafanshi tamkar Nazir Adam Salih
.
Ni dai kun sanni cewa Masoyinsa ne na Hakika , toh yauma ina dauke da wata TSOHUWAR littafinsa wacce ta gama karade facebook da whatssapp, mai suna TSOHON ALKAWARI
.
Labarin wani Dan saurayine mai suna Anas tare da chakwakiyar Soyayyarsa
.
Sunan littatafin kuwa ya samo asaline daga tsohon alkawarin da Nazir Adam Salih yayiwa Tsoho baba sidi mai jakan labarai
.
Nas dai yasaba zuwa wajen bab sidi yana kawo mai tubani shi kuma yana zuba mai labarai toh ayau baba sidi zai bamu labarin ANAS DA MABARUKA GURGUWA
.
Sai ku saurara kuji
.
Anas dai wani kyakkyawan saurayine wanda ya kwarance wajen yaudarar yan mata,
.
Duk da cewa anas ya kasance talaka kuma mai aiki a oTal hakan bai hanashi yana dan kashewa mata kudi
.
MABARUKA hamshakiyar Attajira wacce duk africa babu mai kudinta yarinyar akwai dala sai dai kuma tana da cikas daya zuwa biyu
.
Da farko dai mabaruka Mummunace don kuwa mahaifinta ta biyo sannan ita an haifeta da shanyewar kafafu hakan yasa kullum tana keken guragu
.
Tunda mabaruk ta kyalla ido ta ga Anas sai ta fadawa mahaifiyarta ALIYA cewa ita babu wacce takeso sai ANAS
.
Nan da nan ALIYA ta sami anas sannan ta fadimai bukatunsu, muddin ya auri mabaruka sannan ya kula da ita toh zata sai mai gida sannan ta bashi manaja a kamfaninta, bayan wannan zata zuba mai makudan kudade a account nashi , sannan kowanne Rana zata dunga biyanshi Albashin makuden kudade wayanda adadinsu baya kirguwa
.
.
Ganin wannan daula tasa anas ya zauce nan da nan ya yarda akan cewa zai auri mabaruka giurguwa
.
Toh saidai a inda chakwakiyar take shine aranar bikunsu ne ANAS ya kyallara ido yaga wata kawan mabaruka kyakkyawa ta gaban kwatance nan da nan yaji yana matukar kaunarta
.
TOH tambayar anan shin yaya za'a kaye ne ,
Shin wannan aure zai dore kuwa
.
Ga kadan daga cikin littafin
•••••••••••••••••••••••••••••••••
SIDI MAI JAKA ya dubi kwanon
tubanin dake gabansa ya dubeni
cikin murmushi, sannan sai ya
tura tsinke ya tsikari wani
dankareren tubani ya tura a baki.
"Nas duk duniya babu abin da na
fi so kamar tubani"
"Haka ne" Na ce dashi. Sidi mai
jaka ya dubeni.
"Me yiwuwa ka yi mamakin irin
yadda nake ta zubo maka labari
bana ko tsayawa" Na gyada kai.
"Kwarai kuwa" Na ce dashi
"Domin a wancan karon da na zo
duk kusan mintuna goma sai ka
tsaya"
Sidi mai jaka ya fashe da dariya.
Sannan ya sunkuyar da kai ya ce.
TSOHON ALKAWARIN da ka cika
min ne ya sa nake ta kwararo
labarin nan ba wakafi balle aya"
Na dubeshi cikin mamaki.
"Wane tsohon alkawari kuma?"
Sidi Mai jaka ya dubi kwanon
dake gabansa ya ce.
"Tubanin da ka yi min alkawari
shekaru biyu da suka wuce shi
nake nufi da tsohon alkawari.
Domin ba duka mutum bane a
wannan zamanin kan iya cika
alkawari" Sidi mai jaka ya dan yi
shiru sannan sai ya dubeni ya ce.
"Nas, ina son ka dauki zuciyarka
cancak ka mayar da ita shekaru
ashirin da takwas da suka wuce
a lokacin ma ba a haifi Mabaruka
ba" Na dago da kai cikin kaduwa.
"Shekaru ashirin da takwas?" Sidi
mai jaka ya gyada kai.
"Kwarai kuwa, domin shi ne
zaren labarin mu na biyu." Ya dan
yi shiru kana ya tsikari tubani ya
jefa baki sannan ya dubeni.
"Nas, shekaru ashirin da takwas
da suka wuce, wasu ma'aurata
guda biyu wadanda ke cikin
tsananin shauki na kaunar
junansu sun kasance zaune a
wani fankadeden falo na alfarma
wanda a takure zai iya cin
mutune sittin ba tare da wani ya
shaki numfashin dan uwansa ba.
A zaune a daya daga cikin
kujerun wani mutum ne dogo,
baki, sanye da farar riga suwaita
da shudin wanda na shadda,
kansa babu hula, hakan shi ya
bayyana matashin sankonsa a fili,
da yawa daga cikin wadanda
suka sanshi a lokacin, sun riga
sun yi imani da cewa mutumin
ba zai dade da gashi a kansa ba,
domin gashi dai a lokacin bai fi
shekara talatin da biyar ba a
duniya, amma dogon sankon ya
gama cinye rabin gashin kansa.
Wannan dogon sanko dake kan
mutumin bai hana matarsa Aliya
mutuwar kaunarsa ba, duk kuwa
da cewa a lokacin ma tana da
cikin dan wata takwas Wannan
mutum mai dogon
sankon sunansa A. Faruk. Ba
karamin mutum bane, domin a
fagen kudi biloniya ne,
mamallakin kamfanoni ashirin da
takwas a nan kasar. Jita-jita
kuma na cewa wai yana da
kamfanunnuka sama da goma a
kasar Amurka, da kuma wani
katon asibiti a kasar Birtaniya.
Lokacin da ya auri matarsa Aliya
tana yar shekaru ashirin daidai.
In ban da yawan maganganu n
yan uwa da babu abin da zai sa
ya yi aure a lokacin. Domin tun
yana dan saurayi kafin ya yi arziki
ya taba neman wata yarinya
Murja, wani direban mota ya
kasa shi, tun daga wannan bai
kara sha'awar ya nemi wata
mace ba a duniya sai da ya hadu
da Aliya.
Da farko sa'ar da aka yi bikinsu
da Aliya bai taba tsammanin
auren zai sami wata kyakkyawar
nasara ba. To amma kwanaki
uku kacal da yin auren sai ya
fuskanci ashe Aliya mace ce ta
gari mai iya kissa da soyayyar
janyo hankalin maza. Wannan ita
ta sa a yanzu A. Faruk yake
mutuwar kaunar matarsa Aliya.
Duk inda zashi koda kasashen
ketare ne tare suke tafiya, to
amma yanzu da yake cikinta ya
tsufa sun fi wata uku a gida
Najeriya suna renon cikin.
Aliya ta muskuta akan kujerar ta
shafa cikinta ta ce.
"Kwanta Mabaruka yar gata." A.
Faruk ya ajiye jaridar dake
hannunsa kana ya shafi dogon
sankonsa ya dubi matarsa Aliya
cikin murmushi.
"Aliya, ke fa wallahi ba kya
rabuwa da rigima in ban da abin
ki wa ya ce dake mace za ki haifa
da har ki ke sanya mata suna
Mabaruka?" Aliya ta harareshi,
sannan ta mike da kyar, ta nufo
inda yake, tana zuwa sai ta
kwanta akan cinyarsa a rigingine
kana ta shafo cikin nata ta
dubeshi ta ce a tausashe.
"Ni na san mace ma zan haifa in
Allah ya yarda." Faruk ya fashe da
dariya ya dubeta.
"To yanzu da har ki ka sa mata
suna Mabaruka idan kika haifi
namiji kuma me za ki sa masa?
Kamata ya yi ki zabi sunaye biyu,
na mace da na namiji, ina ganin
zai fi kyau idan namiji ne mu sa
masa suna Mabaruki."
Aliya ta fashe da dariya.
"Kai (darling) don Allah ka daina
sa ni dariya, kar ka sa cikina ya yi
ciwo." Faruk ya dubeta.
"A'a, to ke kin ga laifina? Tun da
dai kin ce idan mace ce za ki sa
mata Mabaruka ni kuwa idan
namiji ne sai in sa masa
Mabaruki." Aliya ta kamo
wuyansa cikin dariya ta matso da
fuskarsa kusa da tata, ta dora
bakinta akan kunnensa ta ce.
"Kai a tunaninka idan na haifi
mace da wa za ta yi kama?"
Faruk ya dan dago kansa sama
ya dubi kyakkyawar fuskar Aliya,
sannan
Faruk ya dan dago kansa sama
ya dubi kyakkyawar fuskar Aliya
sannan ya tuna da dogon
sankonsa, gami da tababben
hancinsa wanda sau da yawa, shi
yake hana shi ganin madubi, sai
ya dubeta da murmushi ya ce.
"Ina fatan ko mace, ko namiji za
ki haifa Allah ya sa ya yi kama da
ke Aliya. Aliya ta rungumo shi
cikin farin ciki domin ita kanta ta
san kyakkyawa ce.
Anan, sai Sidi Mai Jaka ya yi shiru,
sannan ya sa hannu ya goge
gumin da ke sartu akan
goshinsa. Me yiwuwa zafi ne,
babu mamaki kuma zazzafan
yajin tubanin ne ya sashi gumi.
Sidi Mai Jaka ya dubeni ya ce.
"Nas, wani sa'in matasan mata
sukan bani mamaki, da zarar sun
sami ciki sai kaga suna ta zaben,
wai sun fi son su haifi mace, ko
namiji ko kuma mai kama da su,
ko kyakkyawa...hak a dai za ka ji
suna ta kawo tsarabobi iri
daban-daban kai ka ce su ke da
ikon halitta. Ni a ganina Nas, gara
a bar wa Allah zabi domin shi ne
gwani akan komai ko kuwa me
ka gani?" Na gyada kai cikin
sauri.
"Haka ne. Ci gaba baba." Sidi mai
jaka ya dubi kwanon tubanin
dake gabansa kana ya girgizaq
kai cikin takaici, domin duk
yawan tubanin nan dake ciki ya
nhadidiyesu kamar zakara
wadanda suka rage basu fi
kwaya goma ba. Sidi Mai jaka ya
canki na goman karshen ya jefa
baki kana ya ci ga.
"Nas, wata guda da yan kwanaki,
da faruwar wannan hira da na
baka labari dazu tsakanin
ma'auratan biyu, sai Aliya ta
haihu. Ta wani bangaren
haihuwar ta zo musu kamar
yadda suka zata tun farko to sai
dai kuma ta wani bangaren
haihuwar ta zo musu a murde,
musamman ma Aliya. Lokacin da
Aliya ta haihu bata san inda
hankalinta yake ba, sai bayan
kusan sa'a guda da haihuwar ne
sannan likita ta zo gabanta da
murmushi ta ce.
"Ina taya ki murna kin haifi
mace." Aliya ta yi matukar farin
ciki da jin cewa mace ta haifa,
amma sa'ar da likitan ta miko
mata jaririyar da ta haifa sai
duniyar jin dadin Aliya ta birkice
lokaci guda. Aliya ta dubi jaririyar
cikin kaduwa, ko kusa ko alama
jaririyar bata yi kama da ita ba,
gashi dai lafiyayyace sosai to
amma irin tabebben hancin
mahaifinta ya mamaye kusan
rabin fuskarta, bugu da karin
bakin ciki ga Aliya kuma jaririyar
ba ta da kafafu domin duk a
shanye suke sili-sili kamar
maburgi.
"Wannan...kafaf un nata ba za
su
gyaru ba?" Aliya ta tambayi likitan
muryata na rawa. Likitan ta
girgiza kai cikin jimami.
"Babu wani likita a duniya da ya
isa ya gyara kafafun nan nata. Ki
godewa Allah da ya kawota
duniya cikin koshin lafiya, ba kya
ganin idan ki ka dauke
shanyayyun kafafun lafiyarta
kalau." A daidai lokacin da likitar
ta yi shiru sai jaririyar ta bude
idanu. Aliya ta dubeta tayi kamar
za ta fashe da kuka
Ga mamakinta sai jaririyar ta
dubeta ta washe baki cikin
murmushi Aliya ta rungume yar
jaririyarta cikin kuka ya ce.
"Ina son ki Mabaruka, ina son ki
haka nan domin haka Allah ya so
ya gan ki."
Shekaru ashirin suka shude
kamar wasa, a cikin shekaru
ashirin din nan babu irin gatan
duniyar da Mabaruka bata gani
ba. Anan Najeriya ta yi
makarantar firamare dinta,
amma duk sauran karatunta a
Burtaniya ta yi.
Duk da kasancewar Mabaruka
gurguwa kuma mummuna,
iyayenta basu ki nuna mata
tsananin soyayya ba. Wani Ikon
Allah kuma tun daga kan
Mabaruka, Aliya ba ta sake
haihuwa ba, wannan shi ya kara
tsananin kaunarsu a gare ta.
Mabaruka ta tashi cikin jin dadi,
da gata marar misaltuwa, ga ta
dai gurguwa amma duk satin
duniya sai ta hada hadaddiyar
liyafa, wani sa'in kuwa sai ta tara
guragu irinta, ta sa su bi layi a
kofar gida, ita ko a yi ta turata
akan keken guragu na
musamman tana raba musu kudi,
tufa, ko abinci. Kudi ba matsalar
Mabaruka bane, domin
mahaifinta Alhaji Faruk biloniya
ne, ya gama tara mata su gashi
kuma ita kadai ce bata da ko kani
guda daya. Wata rana Mahaifinta
ya taba cewa da ita.
"Mabaruka, duk abin da ki ke so
ki yi da kudi ki yi kawai kar ki ji
tsoron komai ki yi ta kashewa
tun da dai naki ne. Ki godewa
Allah da ya yi ki gurguwa da uba
biloniya."
Mahaifin Mabaruka ya mutu tana
da shekaru ashirin da hudu a
duniya, sakamakon wani
mummunan hadarin jirgin kasa
da ya ritsa da shi a kasar Indiya.
Mahaifin nata Faruk ya bar
duniya da bakin cikin har Allah ya
karbi ransa bai ga mijin yar sa
abar kaunarsa Mabaruka ba. Sau
da yawa ya kan so ya tambaye ta
shin ko ta sami saurayi To amma
idan ya tuna da yadda take ita ba
kyau ba a fuska hakan nan ga ta
gurguwa sai ya yi shiru domin ko
kadan bai san ya yi abin da zai
sosa mata rai Duk da haka nan
sau da yawa ya kan yi alfahari da ita domin ta yi matukar kama
dashi musamman ma tababben
hancinsa mai kamar begila.
Sa'ar da mahaifinta ya rasu, sai
duk kusan kamfanunnukansa da
makudan kudinsa gami da
sauran muhimman kadarorinsa
suka koma karkashinta. Cikin
kankanin lokaci ta zamo tabani
ka ga sarki, ga ta dai gurguwa
kuma mummuna, amma fuskarta
ta fi komai kyau ga duk wanda
ya santa a zahiri da badini ba
don komai ba kuwa sai don
dimbin arzikinta.
Lokacin da mahaifin Mabaruka ya
cika shekaru hudu da rasuwa, sai
mahaifiyarta Aliya ta yi kiranta
wata rana da yamma ta ce da ita.
"Mabaruka kina tunanin aure
kuwa?" Mabaruka ta sunkuyar da
kai cikin taraddadi, domin ta san
tun da take wani saurayi bai taba
dubanta a matsayin ta burgeshi
ba, sai dai ya dubeta a matsayinta na macen da ta fi
kowa arziki a cikin matan Afirka.
"Ina yi." Ta ce da mahaifiyarta
kanta a sunkuye. Aliya ta dubeta
cikin tausayi, domin ta san ko ita
da ta sha miya a duniya ta fi
Mabaruka kyan gani a fuska.
"In dai kin sami wanda ki ke so
sai ki sanar dani, kin ga ke kadai
nake da ita a duniya, shi yasa
nake matukar son na ga jikokina
a duniya tun ina da sauran
numfashina."
Mabaruka ta yi shiru tana
sauraren mahaifiyarta, yanayin
fuskarta a birkice. Ita kanta ta
san mummuna ce, sau da yawa
in ta kalli madubi sau daya ba ta
son ta kuma kallo a karo na biyu,
amma ta kan gode Allah da ya yi
mata dimbin dukiya. Aliya ta yi
nazarin fuskar yar ta na tsawon
lokacin sai ta ga duk hankalinta
ya tashi. Ta san abin da ke
damunta dan haka sai ta dubeta
da murmushin karfafa gwiwa ta
ce.
"Kada ki damu da yadda Allah ya
yi ki Mabaruka, abin da nake so
ki kula shine kina da dukiya, kin
san kuwa a wannan zamanin ba
ta da na biyu." Ta dan yi shiru
tana nazarin fuskar Mabaruka.
"Ina fatan kuna fahimta ta?"
Aliya ta ce da ita tana dubanta
ido da ido.
Mabaruka ta girgiza kai a
sanyaye. Akwai alamun kwalla a
idanunta. To amma bata bari
mahaifiyarta ta gane ba domin ta
san hakan na iya tayar mata da
hankali.
"Abin da nake so da ke Mabaruka
shi ne ki duba ki waiga, ki hanga
da idanunki, duk fadin garin nan,
idan kin hango namijin da ki ke
so, ki ka ga ya kwanta miki a rai
ko wane ne shi ki yi kokarin ki
shawo kansa ya zo nan gida
gurina!" Mabaruka ta dubi
mahaifiyarta cikin kaduwa ta ce.
"Mama...ya ya za a yi na iya kawo
shi har gida? Sai dai in shi ne ya
ganni ya zo ya ce yana sona."
Aliya ta dubeta gami da dariya.
"Mabaruka kenan. Na fahimci har
yanzu ba ki san irin yadda
mutane suka dauke ki bane. To
bari in fada miki duk kasar nan
ke ake labari saboda tsabar
kudin da ki ka gada. Duk da
yadda ki ke ganin ki din nan ki ke
raina kanki kin fi karfin raini,
domin kudinki ya wanke duk
wani nakasu naki. Saboda haka
ina son ki sani cewa babu wani
da namiji da za ki kirawo a girin
nan ya ki zuwa gare ki ko shi
wane ne, domin kina da babban
makamin da ya fi nukiliya tasiri,
dan in ba kudi babu zancen
nukiliya balle aikinsa." Aliya ta
dan yi shiru tana duban fuskar
Mabaruka sannan sai ta daga
hannu ta nuna fuskarta ta ce.
"Na baki daga nan zuwa sati
guda duk namijin da ki ka gani
ya yi miki ki yi kokarin ki kawo
min shi nan..
•••••••••••••••••••••••••••••••••
Domin jin karashen wannan labari daga bakin baba sidi mai jaka
sai kuyi marmaza ku download na littafin zuwa kan wayoyinku ta hanyar danna wayannan blue din Rubutun
.
DOWNLOAD AS PDF EBOOK
DOWNLOAD AS TXT EBOOK
DOWNLOAD AS EBOOK
Kar dai ku manta :- littafin kala Uku ne akwai PDF,TXT da DOC sai ku zaba wanne manhaja kuke so kokuwa wanda zai iya budewa acikin wayoyinku ko kwamfitarku
.
.
Ga duk wanda yasan bai iya download na ebooks a shafina ba sai ya shiga nan yayi mani magana http://keffians.xtgem.com/forum
.
Sannan ina Gargadi
Ni bana Tura littafi a biyani sai dai inkaine da kanka kaga daman turomani da kudi don Allah
Bana saida Littafi a internet, domin sha'awa kadai nake hada ebooks don masu karatun hausa
.
Sannan bana whattsapp kuma bani da group a whattsapp
.
Kada wani ya ha'inceku ta hanyar amfani da Sunana a whattsapp
.
TSOHON ALKAWARI complet
Na Nazir Adam Salih
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so
For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521
Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) nazir adam Salih
Bissalam daga Shuraih Usman 99%
0 Response to "TSOHON ALKAWARI complet na NaZir Adam Salih"
Post a Comment