KUDI DA MACIJI complet na NaZir Adam Salih
Sunday, 12 August 2018

KUDI DA MACIJI
Hausa ebooks
Nazir Adam Salih (m)
Made:- Shuraih Usman
Shuraih 99%
•••••••••••••••••••••••••••••••••
Assalam jama'a ayau dai ina tafe maku da wata tsohuwar littafin Nazir Adam Salih wanda tayi tashe a facebook da ma wasu kafafen sadarwa irinsu whatssapp mai Suna KUDI DA MACIJI
.
Wannan e-book din tana tattare da darussa masu tarin yawa wanda innace zan tsaya zayyane su anan toh sai in cike description din ban ban kare ba
.
A shekaru dari da ashirin 120yrs da suka gabata ne Wani SARKIN BARAYI mai suna ZANGERU tare da abokansa biyu Mai masaba da makwara suka yi wani gagarumin Sata
.
Wannan sata dai itace sila ta abubuwa da yawa,
Wannan satar tayi silar Rasa rayuka da dama ciki kuwa har da rayukan su kansu barayin
.
Amma kafin Zangeru ya rasu sai da ya kira wata Aljana ya bata dukkan dukiyar ta boye masa sannan ya rubuta wa dansa AMADI wasiyya akan dukiyar , ya baiwa wannan Aljana ta kaiwa mATARsa TAGOGARI
.
Sai dai Kash koda aljanar ta baiwa tagogari wannan wasiyyar ta kuma fada mata mijinta ya rasu, sai tagogari ta zata ko wasiyyar nan LAYACE ,
.
Hakan yasa ta baiwa danta Amadi wasiyyar a amatsayin layar maganin tsautsayi, kafin ta mutu
.
Toh dukiyar da su zangeru suka sata dai dukiyar budurwar yaron zangeru ne Amadi, shi kuwa amadi sai ya bawa budurwarsa wannan laya amatsayin maganin tsautsayi
.
Kai dai in takaice maku labarin sai da layar nan tayi shekaru dari da ashirin 120yrs awuyan zuri'ar Zangeru , a matsayin maganin tsautsayi, haka wannan laya ta runga shude zamani,
.
Wannan ya gada a wajen babansa, ya baiwa dansa, har wata yarinya mai suna Aisha ta gaji Layar a wajen mahaifinta
.
Duk da ya kasance AISHA tana cikin matsanancin talauci, kuma ta tsani wannan laya,
.
Cikin sa'a sai wannan Aljanar ta fito wa aisha ta bayyana mata sirrin Layar cewar ba laya bace Wasiyya ce
.
Hakan yasa aisha da saurayinta shafi'u suka dauki aniyar nemo wannan dukiya mai tarin yawa a wannan duniya
.
Toh shin zasu samu nasarar samun dukiyar,
.
Wacce irin cakwakiya zasu shiga
.
Ga kadan daga cikin littafin
••••••••••••••••••••••••••••••••
Lah. Kaga dogayen duwatsun nan da baba yasha bamu labari hussaina tace da dan uwanta hassan cikin doki lokaci guda kuma ta mike hannunta daga kan dokin ta taba dutsen da kyawawan yatsunta.
Hasssan ya dubi dutsen a yatsine sannan ya dubi yar uwar tasa hussaina yace kinga nikuwa babu abinda na tsana a rayuwata irin dogayen duwatse.
Meyasa? Hussaina ta tambaye shi gamida murmushi domin ta riga tasan tafi dan uwan tagwaitakar tata jarumta.
Kawai dai ni banason ganin dogayen duwatsu ne banayi wata sa'ar dai inga kamar mutuwa ce ke kokarin zuwa ta zare ni musamman ma a irin wannan lokaci na Duhu.
Hussaina ta bushe da dariya kaidai wallahi matsoraci ne in ba haka ba kataba ganin an gujewa mutuwa?
Ai duk inda kwananka ya kare ko a kan duwatsu ko acikin fadar babanmu sarki ko acikin duhu ko hasken rana sai mutuwa ta riske ka domin idan tazo babu tsimi babu dabara.
Hassan ya dubi yar uwarsa da murmushi cikin duhun daren wannan gaskiyane yar uwata Hussaina.
Sarkin dogarai dake daf dasu yayi murmushi acikin duhun daren sa'ar dayaji hirar dake gudana atsakaninsu sannan kamar yadda ya saba fadi akullum cikin zuciyarsa yanzu ma sai yace INAMA ACE 'YA'YANSA NE.
Sarkin dogarai ya juya baya ya dubi yan rakiyar tasu mutum shida kowannensu cikin shigar yaki dauke da kibai masu dafi suna tafe suna sa kakkafar dokin da aka dorawa akwatin dukiyar atsakiya wata sa'ar ko motsin ganye sukaji sai sun juya da shirin kai sara kamar MACIZAI.
Duk da wannan shiri da barazana da sukeyi basu taba tsammanin wani abu makamancin fashi zai faru akansu ba domin sunyi imani da cewa duk wani barawo dake hanyar yasan da irin jarumtar ta baraden sarki a tunaninsu babu mai iya tunkararsu da wata barazana.
Mutanen duniya basuda tabbas suna iya baku mamaki sarkin dogarai Hambara yace dasu sa'ar da zasu baro gida.
Wannan shi yasa baraden yan rakiya daukar takubba sabanin kwari da bakan da suka dauka tun farko acan gefe guda kuma bayan....Wannan shiyasa baraden yan rakiya daukar takubba sabanin kwari da bakan da suka dauka tun farko.
Acan gefe guda kuma bayan duwatsun cikin duhu makwaro ne zaune yana dana kibiyarsa ta farko wacce da itace yake fatan mika sarkin dogarai lahira tare da sauran jama'arsa. Acan kuma karshen duwatsun sarkin barayi zangeru ne shida abokinsa sarkin makera da barayi mai masaba sunyi kwanto suna jiran karasowar tawagar ayarin tun farkon shigowar almuru suke nan makale har sun fara kosawa saboda tsabar rikon kibiyar a dane har hannun zangeru ya fara gumi
suna nan makale lokaci kuma suna makyarkyatar sanyin asuba da yafara hurowa wata sa'ar jikinsu har buguwa yake dana juna kamar zakarun da ruwa ya jika.
Adaidai wannan lokacin ne suka jiyo motsin ayarin tawagar sun doso inda suka boye mutanen biyu sarakan barayi suka dubi juna lokaci guda kuma suka hangi inda makwaro yake make daga inda suke zaune suna iya hango rungumemen kan makwaro wanda ke zaune yayi dani baya ko motsi kamar gunki.
Allah yasa kada lalataccen can ya harbi yaran nan biyu...zangeru yace batareda ya dubi mai masaba ba domin tuni har sun fara jiyo hayaniyar mutanen suna hira.
Ai kuwa in ba wata sa'a ba da nisan kwana sai ya kashe su kaga dai sana'ar mu daya dashi amma wallahi ni kaina tsoron rashin imaninsa nakeyi.
Zangeru yaji wani gumi yafarayi masa sartu a doron baya harga Allah bashi son abinda zaisa a kashe kyawawan 'ya'yan sarkin nan domin shi dukiyar ce kawai agabansa ba kisan kai ba.
To sai fa garemu gasu nan sun matso mai masaba yace da zangeru sannan cikin zafin nama na ban mamaki sai ya gyara danin kibiyar dake jikin bakansa sannan ya cilla harbi cikin ayarin ta tsakanin duwatsun ba'a dade ba sukaji an kwalla kara mai tsanani sannan sai sautin fadowar wani abu mai sauti irin na buhun sumunti.
Na sami daya kafiri. Mai masaba yace cikin karaji.
Zangeru jiki na rawa ya shafi gefen tsafaffen bantensa inda ya kulla duwatsun nan da balbale ta bashi ya tabbata yana nan sannan sai shima ya cilla harbi cikin ayarin nan da nan hayaniya ta barke da hargowa da ife ife cikin razana da kaduwa daga cikin duhu zangeru ya hangi makwaro ya fara cilla harbi cikinsu har sau uku duk harbin dayayi sai ya jefa mutum daya kasa.
Ba'a dade ba sai wajen yayi tsit bakajin komai sai gurnani da motsin dawakai mai masaba ya dubi zangeru jikinsa na rawa yana haki yace Munci Nasara... Lalataccen duk ya kwantar dasu.
Zangeru bai ko dube shi ba jikinsa sai kyarma yakeyi abinda ke damun zuciyarsa shine kyawawan yaran ya'yan sarki ko shakka bayayi makwaro duk ya harbe su yakuwa tabbatar kibiyar makwaro tsafaffiya ce bata sukar mutum ya rayu ga mamakin zangeru sai yaji a karo na farko ya tsani kansa ya kuma tsani makwaro don me? Don me awane dalili zai kashe wannan kyakkyawar budurwa ita da dan uwanta bayan shi kuma nasa dan Amadi yana can gida lafiya kalau babu ko kwarzane ajikinsa?
Wayyo Allah na shiga uku na lalace Hassan ihun hussaina ya ratsa cikin dajin amsa kuwwar ta watsu cikin duwatsun sarakan barayin biyu suka dubi juna sannan lokaci guda suka dubi inda makwaro yake kwatsam sai sukaga ya mike tsaye ya zaro kibiya daga cikin kwari ya danata sannan sai yayi awon cikin duhun inda sukaji ihun farko.
Zangeru zuciyarsa ta harba domin yasan abinda makwaro yake nufin yi cikin zafin nama na mamaki sai zangeru ya dana kibiyar ya saita wuyan makwaro ya harba kamar wasa sai kibiyar ta sami inda aka yi nufinta makwaro ya kwalla ihu sannan sai yafi agurin.
Mai masaba ya dubi zangeru cikin kaduwa yace Haba zangeru kanka daya kuwa meyasa zaka harbe shi?
Zangeru ya harari mai masaba acikin duhun yace a fusace meyasa zai kasheta bayan kuma da sauran kwananta a duniya? Ko ya dauka shi kadai yake da tsafin harbi? Yau kunama ne shi nakawo karshen karyar banza.
Mai masaba cikin kaduwa ya mike tsaye a fusace bazatayi ba zangeru dole ne mu kashe yarinyar nan tunda sauran sun mutu dole ne itama ta mutu idan kai bazaka iya taba ta ba bari ni in tafi kasa na karasa ta.
Yana gama fadin haka sai yafara gangarawa kasan dutsen ya nufi inda suka jiyu ihun budurwar adaidai wannan lokacin ne zangeru yaji kamar wani abu na sukansa a kugu cikin sauri ya yakai hannu gurin sai yaji ya taba tsinken kibiya jikinsa na rawa ya zare kibiyar daga kugunsa ya dagata sama cikin duhun daren ko shakka bayayi daga cikin kibiyoyin da baraden sarki suka sami damar harbowa ce ta huda bantensa ta kuma dan soke shi kadan a kudu babu mamaki tashin hankali ne ya hanashi jin sukar kibiyar tun farko.
Zangeru yayi kamar ya jefa da kibiyar daya zare daga kugunsa can kuma sai ya fasa lokaci guda kuma yaji wani zazzafan gumi ya fara wanke masa fuska yasha jin labarin cewa duk kibiyoyin dake kwarin baraden sarki a shurbune suke da masifaffen dafi wanda duk wanda yasoka bazai rayu ba.
Daga inda yake tsaye yana iya hangen faffadan bayan mai masaba wanda ke gangarowa ahankali ta tsakanin duwatsu
Kyakkyawar budurwar yarinya ce karama bai kamata ta mutu tun yanzu ba ni kuwa tawa ta kare kamata yayi mu wuce lahira nida babban abokina. Zangeru na gama fadin haka sai ya shafi kugunsa inda kibiyar ta same shi baiyi mamakin jin gurin tuni har ya fara kumbura ba yaji wani zafi ya soki kugun kamar ana hura masa wuta yanzu kam ya tabba dafi ne ajikin kibiyar.
Zangeru ya jinjina kibiya ahannunsa sannan ya dana ta ya daga bakan sama ya saita faffadan bayan babban abokinsa Mai Masaba sannan sannu ahankali batareda wata nadama ba domin yasan ceton rai yakeyi sai ya saki Kibiyar CUL.
** ** ** ****** ****** ***** *****
Lokacin da zangeru ya dawo bakin katuwar koramar ta danmusa tuni har ya gari yagama wayewa yayi sa'a bai hadu da kowa ba sai wata tsohuwa mai sammakon tsiya dake bayan gari a musissika dake daf da koramar tana shikar gero.
Sannu da zuwa bawan Allah tsohuwar tace da zangeru sa'ar data ganshi tafe bisa katon doki dauke da akwatin karfe yana tafe yana layi kamar zai fado daga kan dokin sakamakon dafin kibiyar dake daukarsa.
Baiko dubi tsohuwar ba ya wuce kai tsaye zuwa can cikin koramar jikinsa na ta rawar dari sakamakon mummunan zazzabin dake addabarsa lokaci guda kuma zuciyarsa na ta tunanin halinda hussaina take ciki.
Lokacin da zangeru ya tabbata ya harbe babban abokin satarsa mai masaba sai ya gangaro daga kan dutsen yana layi yashigo har inda tawagar baraden sarkin suke duk a kwankwance kuma a marmace bayan ya tabbatar babu mai wani sauran numfashi sai ya fara laluben inda Hussaina take ya dade yana lalube kafin ya ganota karkashin wani lankwasashshen dutse mai siffar bil'adama tana kwance a sume zangeru ya jujjuya ta na dan lokaci ya tabbatar suma tayi ba mutuwa ba sannan saiya data ta yayi abinda rabonsa dayayi tun yana karami -- ADDU'A.
Allah sarki kyakkyawa Allah yasa fatake su tsince ki yana gama fadin haka saiya nufi inda dokin akwatin dukiyar yake ya yunkura ya haye bisa dokin ya juya ya kalli gawarwakin kallon karshe sannan sai ya karkata linzamin dokin yabi takan gawar babban abokinsa Marigayi Mai Masaba yakoma da baya.
Don haka ayanzu da zangeru yazo bakin korama sai ya hangi wata doguwar bishiyar giginya dake gangare ba'a nan yaso ya tsaya ba to amma dayake jikinsa yagama yin rauni sai ya sauka agurin baiyi mamakin jin kafafunsa sun kasa daukar nauyinsa ba ahaka yafadi a gurin zaman yan bori bai damu ba domin tuni ya shirya abinda zai acikin zuciyarsa jikinsa na rawa ya lalubi inda ya kulle farin dutsen nan acikin bantensa ya kunto dutsen sannan saiya sa dutsen tsakanin tafin hannunsa biyu ya murza.
GANI ZANGERU ME KAKE SO MASOYINA?
Farar balbelar tace sa'ar data bayyana agabansa
zangeru ya dubi balbelar yana haki bakinsa na rawa yace dan lokacin daya rage min aduniya kadan ne shiyasa na neme ki domin kiyimin taimakon karshe kuma muyi sallama kafin na mutu
''Me kake so?
Zangeru ya dubeta yace kai tsaye so nake ki sa yan uwanki su tona rami yanzun nan su binne min akwatin dake kan dokin nan inason kuma ki kawo min warka(takarda) da alkalami.
''An gama balbela tace sannan ta bace ba'a jima ba saita sake bayyana ita da wani dankareren aljani dauke da tawada da waraka.
'Binne akwarin nan agindin bishiyar giginyar can balbelar ta umarce shi.
Kafin kiftawa da Bismilla bakin Aljanin ya daki saman akwatin da karfi akwatin ya nutse acikin kasa
Ga tawada da takardar balbelar tace da zangeru
hannunsa na rawa yayi rubutu mai tsayi ajikin takardar da AJAMI sannan ya yiwa takardar nadin laya ya mikawa balbelar yace ga wannan ki kaiwa matata kice da ita ni na mutu kuma wannan takardar tabaiwa dana amadi sakone aciki shine kadai gadon da zan iya bar masa aduniya tari ya shaqe zangeru nan da nan yafara bakin amai na dafi ba a dade ba sai idanunsa suka kakkafe akaro na farko arayuwarsa sai zangeru yaji nadama tazo masa to amma duk da haka saiyaji gamsuwa tazowa zuciyarsa tun da dai wai atunaninsa yayi abin kirki akaro na farko ya ceci rayuwar Hussaina da wannan tunanin ya MACE.
Balbelar ta dubi gawar zangeru saita dubi katon bakin aljanin tace zauna anan kayita gadin wannan akwatin daga yanzu har zuwa abinda hali yayi
''An gama ranki ya dade bakin Aljanin ya daki kasa wata katuwar kujera ta hudo kasa ta fito aljanin ya hau kai ya harde sannan yace
YI TAFIYARKI RANKI YA DADE KARKIJI KOMAI NI INA NAN KAFIN ALLAH YA DAUKI RAINA.
Balbelar tayi fir da nannadaddiyar takardar abakinta.
•••••••••••••••••••••••••••••••••
sai kuyi marmaza ku download na littafin zuwa kan wayoyinku ta hanyar danna wayannan blue din Rubutun
.
DOWNLOAD AS TXT EBOOK
DOWNLOAD AS PDF EBOOK
DOWNLOAD AS PDF EBOOK
Kar dai ku manta :- littafin kala Uku ne akwai PDF,TXT da DOC sai ku zaba wanne manhaja kuke so kokuwa wanda zai iya budewa acikin wayoyinku ko kwamfitarku
.
.
Ga duk wanda yasan bai iya download na ebooks a shafina ba sai ya shiga nan yayi mani magana http://keffians.xtgem.com/forum
.
Sannan ina Gargadi
Ni bana Tura littafi a biyani sai dai inkaine da kanka kaga daman turomani da kudi don Allah
Bana saida Littafi a internet, domin sha'awa kadai nake hada ebooks don masu karatun hausa
.
Sannan bana whattsapp kuma bani da group a whattsapp
.
Kada wani ya ha'inceku ta hanyar amfani da Sunana a whattsapp
.
KUDI DA MACIJI complet
Na Nazir Adam Salih
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so
For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521
Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) nazir adam Salih
Bissalam daga Shuraih Usman 99%
0 Response to "KUDI DA MACIJI complet na NaZir Adam Salih"
Post a Comment