JARUMA YAZILA littafi na biyu 2

JARUMA YAZILA littafi na biyu 2
Saturday, 11 August 2018


Kadan daga ciki
Lokacin da jaruma yazila ta hango kofar birnin kisra daga
can nesa, dabara ta fadomata na yadda zata shiga cikin
birnin bisa batar da kamanninta koda wannan dabara
tazo mata sai ta tsayar da dokinta ta sauka, sannan ta
daure dokin agindin wata bishiya. Dama awannan lokaci
rana ta kwalle gashi ta gaji ainun kuma guzirinta ya kare
har ta fara jin yunwa da kishirwa. Ka wai sai yazila ta
shimfida darduma a karkashin wannan bishiya ta
kishingida akai tana tunanin yadda zata shiga cikin birnin
misra. Tana cikin wannan hali ne kawai sai ta hango an
bude kofar birnin, sai ga tawagar wadansu dakaru
kimanin su arba'in sun fito bisa dawakai a cikin shigar
yaki kuma sun durfafo inda take zaune.
Cikin hanzari jaruma yazila tayi girgiza, nan take ta rikide
ta zama tsohuwar mafarauci sanye da walki da rigar fata,
kuma. A rataye da kwari da baka. A kafarsa yana sanye da
ta kalmin fata. A kan dokinsa kuwa tsuntsayene kala-kala
kimanin guda bakwai duk matattu alamar cewa harbosu
yayi.
Nan take dardumar dake shimfide a kasa itama ta rikide
ta zama buzu. tsuhun yana ki shingida akan buzun yana
hutawa
A dai-dai wannan lokaci ne wannan lokaci ne wannan
tawaga tazo za ta gifta ta gaban mafarauci. Koda ganin
wannan mafarauci sai shugaban tawagar yaja linzamin
dokinsa ya tsaya a gabansa. Bawani bane shugaban
tawagar face jaruma dabira. Tana sanye da kayan yaki,
kuma tarufe fuskarta da hular karfe, kofofin idanunta da
hancinta da bakinta kadai ake gani.
Jaruma dabirA ta dubi wannan tsohon mafarauci sama
da kasa tare da karemasa kallo cikin nutsuwa sannan ta
daka masa tsawa tace, "yakai wannan tsohon mafarauci
wanene kai, kuma daga ina ka fito sannan menene ya
kawoka nan kusa da kofar birninmu?".
Da jin wannan tambaya sai tsoho yakama makyarkyata
cikin alamun tsoro yace, 'ki gafarceni yake shugabata
sunana kasim kuma ni bakon mafaraucine na fitone daga
kasar rum. Na shigo cikin dazuzzukan dake kusa da iyakar
kasarku ne da tamu ina farauta sai guzurina da ruwan
shana suka kare shina na zonan na zauna ina hutawa idan
rana tayi sanyi na shiga kasarku na sayar da 'yan
tsuntsayen dana harbo na sami abin da zan sake yin
guzurin na koma kasata".
Koda jin wannan batu sai jaruma dabira tayi murmushi
saboda jin cewa tsohon daga kasar rum yake domin
birnin rum ma'abota addinin musuluncine a wannan
lokaci, kuma akwai alaka tsakanin mutanen birnin Rum
da mutanen birnin Misra.
Dabira ta dubi tsuntsayen da tsohon ya harbo wadanda
ke kan dokinsa taji sha'awarsu domin babu irinsu a cikin
yankin dazuzzukan kasar misra don haka sai ta dubi
tsohon ta ce "yakai kasim nayi sha'awar wadannan
tsuntsaye naka saboda haka ni zan siyesu nawa ne? Kuma
inaso karamu izuwa dajin daka harbo irin wadannan
tsuntsaye domin nima na farauto irinsu domin a halin
yanzu farautar muka fito. Zan biyaka da lada na
musamman idan kayi mana wannan rakiya "
Koda jin haka sai farin ciki ya lullube tsoho kasim yayi
godiya. Nan take jaruma Dabira tasa aka bawa tsoho
kasim abinci da ruwa sha ya cika cikinsa ya koshi, sannan
ya hau dokinsa ya wuce gaba yayi musu jagora izuwa
cikin daji.
A wannan lokaci zuciyar tsoho kasim daka take kamar
zata tsaga kirjinsa ta fado kasa domin bai san dajin da zai
kai su dabira ba su sami irin wadannan tsuntsaye na sihiri
da ya samar dasu.
MEZAI FARU TSAKANIN YAZILA DA DABIRA A CIKIN
WANNAN TAFIYA TA SHIGA DAJI DOMIN FARAUTA?
@SHIN JARUMA YAZILA ZATA CIKA BURINTA BISA ABIN
DA YA KAWOTA BIRNIN MISRA?
@YAUSHENE DABIRA ZATA GANE CEWA YAZILA 'YAR
UWARTACE TA JINI, KUMA IDAN TA GANE HAKAN MAIZAI
FARU ?
@SHIN IDAN HUMAIRA TA HADU DA YAZILA ZATA
SHAIDATA A MATSAYIN 'YAR CIKINTA KUWA ?
@YAUSHENE ZATA KOMA BIRNIN KISRA KUMA IDAN TA
KOMA MAI ZAI FARU?


Domin jin abin da zai faru sai ku downloading na littafin anan


DOWNLOAD AS TXT/ DAUKO SHI A MATSAYIN TXT


DOWNLOAD AS PDF/ DAUKO SHI A MATSAYIN PDF

DOWNLOAD AS DOC/ DAUKO SHI A MATSAYIN DOC

0 Response to "JARUMA YAZILA littafi na biyu 2"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel