TAKOBIN JINI littafi na biyu 2

TAKOBIN JINI littafi na biyu 2
Saturday, 11 August 2018



Kadan daga ciki

Anyi wani hatsabibi kuma jarimin gaske shekaru dubu
shida da suka wuce shi wannan hatsabibin jarumin ya
kasance bokane sunansa MURAISU Muraisu ya gagari
duk wasu jarumai da bokayen nahiyarsu Muraisu na
iya yaki da dakaru dubu sannan kuma ya kashe su
dukkaninsu batare da ya nuna alamun gajiya ba .
Muraisu yana da wata kanwa tasa dayake matukar
sonta wadda itakuma ko kadan bata son halayensa
hakan nema tasa ta tafi ta barshi taje can nisa dashi
tayi aure . Duk da cewa muraisu ya binciko inda take
acikin madubin tsafinsa hakan baisa yaje gareta ba .
Sabida kafin ta tafi ta gargadeshi da kada ya tafi
nemanta . To ayayin da muraisu yaga tsufa tazo masa
sannan wannan tarin kundin ilimin tsafinsa izan har ya
bari wani ya mallakeshi bayansa toh yana iya zama
gagara badau a bayan kasa baki daya wannan tasa ya
sana'anta wani takobi wanda har takaishi tsawon
shekaru biyu sannan ya kammala ta , Wannan takobin
takasance marikinta na jauharine yayin da jikinta
gabadaya anyisane da lu'u lu'u sannan aka gauraya da
Jini wannan shiyasa jikin takobin gaba dayanta launin
jaa ce . Yayin da muraisu ya sana'anta wannan takobi
sai yasa wasu dakaru Dubu dari na Aljanu su tsareta
sannan ya dauki takobin yakaita Kokogon sha jini Ita
wacannan takobi na muraisu yayin da mutun ya
mallaketa toh baza ka taba cin nasara akansaba sannan
kuma wannan ma mallakintan zai mulki duniya gaba
dayanta sabida karfin sihirin dake tattare da takobin
sannan kuma manyan sarakunan Aljanu har su biyar
na ma wannan takobin bauta duk ma mallakin wannan
takobin to zasu kasance masu biyayya agareshi .
Download the full ebook below

DOWNLOAD AS TXT/ DAUKO SHI A MATSAYIN TXT


DOWNLOAD AS PDF/ DAUKO SHI A MATSAYIN PDF

DOWNLOAD AS DOC/ DAUKO SHI A MATSAYIN DOC

0 Response to "TAKOBIN JINI littafi na biyu 2"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel