JARUMA YAZILA littafi na UKU 3
Saturday, 11 August 2018

Kadan daga ciki
Al'amarin yazila kuwa, lokacin da aka kaita kurkuku aka
kulleta sai taji ko kadan bata damu ba face kawai tana
zumudin yamma tayi a fito da ita a kaita filin fada inda
zasu yi yakin keji ita da jaruma Dabira.
Har rana ta take Yazila ta kasa tsaye ta kasa zaune a cikin
kurkukun. A lokacin ne aka kawo ma ta abincin rana. Ko
kallon abincin batayi ba bare ma taci.
Ai kuwa bayan an idar da sallar la'asar da kimanin rabin
sa'a sai aka bude kofar kurkukun aka tasa keyar yazila
izuwa fada. Tana tafe tana jan sarkar da aka daure
kafafunta da hannayenta, dakaru na biye da ita.
Lokacin da aka iso filin fadar da jaruma YAZILA sai taga
filin fadar ta cika makil da jama'a fiye da kullum, harma
mutane sun rasa inda zasu tsaitsaya sai akan katangau.
A tsakiyar fadar kuwa, an ajiye wannan katon kejin karfe
mai tsawo da fadi wanda aka yi masa 'yar karamar kofa
ta shiga.
A can gefe daya kuwa, sarki RAIHAN ne da 'yan
majalisarsa a zaume kuma daf da shi JARUMA DABIRA ce
a tsaye cikin gagarumar shigar yaki fuskarta a rufe cikin
hular karfe kamar kullum.
Koda aka ga anzo da YAZILA sai aka yi sauri aka bude
kofar wannan keji. Cikin hanzari aka kwancewa yazila
sarkokin dake hannayenta da kafafunta aka bata takobi
sannan aka ingizata izuwa cikin kejin. Nan take Jaruma
Dabira ma ta baro inda su sarki suke ta nufi inda kejin
yake.
Koda ganin haka sai fadar ta rude da kabbara aka rinka
yiwa Dabira Jinjina har ta shiga cikin kejin aka rufe kofar
kejin.
A sannan ne aka yi tsit! A fadar gaba daya tamkar mutuwa
ta gifta. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin jaruma
Dabira da Jaruma YAZILA.
Jaruma Dabira ta dubi yazila cikin murmushi tace, "yau
mun hadu a inda babu damar gudu, kuma babu
yankewar yaki face dayanmu ya sami nasara akan daya.
Ina so ki sani cewa tuni na kona gaba dayan layoyinki da
gurayenki na tsafi yanzu dame kuma za kiyi dogaro?".
Koda jin wannan tambaya sai Yazila ta bushe da dariya
tace, "ke yarinya, aikin kashe micijine baki sare kansa ba.
Kin ga wannan laya dake wuyana wani malami ma'abocin
addininku ne ya bani ita bayan an bashi dukiya mai
tsananin yawa. Kuma ya tabbatar mini da cewa in dai ina
tare da ita babu wani mahaluki daya isa ya sami nasara
akaina ".
Koda jin haka sai Dabira ta fusata ta zare takobinta ta
afkawa yazila suka ruguntsume da azababben BAKIN
ARTABU wanda ya dugunzuma hankalin kowa a wajen,
domin su biyun babu wanda ke da alamun samun nasara
akan abokin gwaminsa.
WAYE ZAI SAMU NASARAR WANNAN GAGARUMAR
HADUWA DA AKAI ?
SHIN DABIRA ZATA CIRE LAYAR WUYAN YAZILA ITAKUMA
TA CIRE HULAR KANTA?
IDAN SUN SAMI NA SARAR HAKAN ME ZAI FARU ?
YAUSHE ZA A KWABSA YAKI TSAKANIN RUNDUNAR
BIRNIN KISRA DA RUN DUNAR BIRNIN MISRA?
A WANNE HALI HUMAIRA MAHAIFIYAR DABIRA TAKE
CIKI?
SHIN DABIRA DA YAZILA SUNA GANO CEWA SU 'YAN
UWAN JUNANE ? IDAN SUN GANO ZASU JE DAUKAR
FANSA ABIRNIN KISRA AKAN SARKI DAKSUR?
Dauko cikakken littafin Anan
0 Response to "JARUMA YAZILA littafi na UKU 3"
Post a Comment