NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 na Shuraih Usman

NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 na Shuraih Usman
Saturday, 11 August 2018



Kadan daga ciki

Sarki humaiz yace toh shin yanzu ina mafita, .
Boka kamsusuljani yace" mafita dayace " Cikin kaguwa
sarki humaiz yace "yakai dirkan birnin tehran gaggauta
sanar dani mafitar da ka samo mana" . Boka yace
"bakomai bane wannan mafita face ka mallaki Wata
KAMBUN TSAFI wacce aka killace ta a tsibirin bahar
jallus" . Boka kamsusulajani ya dubi sarki Humaiz bin
Humas yafara bashi labari kamar haka . Kimanin
Shekaru aru aru da suka shude A Cikin wannan birnin
Na Tehran anyi wani gawurtaccen Azzalumin sarki mai
suna LU'UMANU na birnin Tehran a duba KUNDIN
TSATSUBA . Shi wannan sarki mai suna Lu'umanu yana
da wata kambu na tsafi wacce take daure a hannun
hagunsa, Da wannan kambune yayi amfani inda yai ta
shimfida mulkin zalunci , Har lokacin da wani
ma'abocin bakon Addini ya hallakashi . Yanzu kambun
tsafin na ajiye a tsakiyar tsibirin bahar jallus, Muddin
ka mallaki wannan kambu toh duk duniya babu wani
jarumin da bazaka taka ba, Sai ka zama guguwar
Annoba mai shafe birane, Akwai wasu Manya manyan
sarakunan aljanu na duniya baki daya guda goma sha
bakwai da ke ma wannan kambu bauta, Muddin ka
mallaki wannan kambun toh duk zasu da wo karkashin
ikonka, . Ita wannan kambu tana tattare da alkaluman
sihirin tsafi guda dubu Kasani muddin ka mallaki
wannan kambu toh tamkar ka mallaki wayan can
sihirin tsafin ne, , A baya jarumai, sadaukai, da Mazan
kwarai, duk sun rasa rayukansu bisa mallakar wannan
kambu ta tsafi, . Kayisani yakai wannan sarki Kafin ka
isa tsibirin bahar jallus kuwa sai ka bita cikin wasu
mugayen dazuka guda biyu, . Dajin farko ana kiransa
da suna Burkum Babu komai acikin wannan daji face
dandazon yan fashi wayanda adadinsu yafi milyan Su
wayannan yanfashi sun kasance mugayene sam basu
da imani ko kadan don ko bera sukai arba da ita toh
take suke gutsutstsure namanta su rabata ga junansu
yadda kowa sai ya samu . Komai suka samu raba
daidai suke da ita yadda kowa zai samu duk
kankantashi kuwa, . Atarihin wannan daji babu wani
mahaluki walau mutum ko aljan wanda ya taba
ratsawa ta cikin wannan daji a raye, Kai muddin
mutum ya shiga wannan daji toh tamkar ya shiga
lahira ne don kuwa baza a sake jin duriyarsa ba . , Daji
na gaba kuwa ana kiransa Da suna Darul marid babu
komai acikin wannan daji face wasu irin zabga zabgan
maridai wayanda adadinsu yakai dubu . Su wayannan
maridai kaifi ko tsini baya tasiri ajikinsu face zagwaron
karfin damtse, don sun kasance suna masu baiwa
jikinsu horo ta hanyar shan wani tsumi wanda muddin
suka sha toh ko kwana zakayi kana saransu , Ba za su
san kanayi ba . A tarihin duniya baki daya ba'ataba
samun wanda ya ratsa ta cikin wayannan dazuka guda
biyu sannan ya fito a raye ba walau mutum ko aljan, .
Shi kuwa tsibirin bahar jallus, duk yafisu masifa da
bala'I Don kuwa wasu irin Aljanu ne a wajen Su
wayannan aljanun suna da katon kai kaman randa
sannan sai sililin kafafuwa wanda ke barazanar
karyewa a ko wani lokaci, , Aljanun gaba daya
jikkunansu launin ja ne, Da sun hadu da mutum ko
aljan nan take zasu zuke jinin jikinsa, ta hanyar taba
sassan jikinsa . Su wayannan aljanu suke tsaron
wannan Kambu ta tsafi . Lallai tafiya neman wannan
kambun tsafi bakaramin masifa da bala'I bane Don
kuwa NAMIJIN GASKE ne kadai zai iya tunkarar
wayannan masifu batare da yaji tsoro ko shakka acikin
zuciyarsa ba ." Koda boka kamsusuljani yazo nan
azancensa sai yaga sarki humaiz ya bushe da dariya
al'amarin daya bashi mamaki kenan Sarki humaiz ya
dubi boka kamsusuljani cikin yarda da kai yace "Lallai
ko zan rayuwata sai na mallaki wannan kambun tsafin
kuma ina sanar dakai cewa ka shirya don kuwa da kai
za'ayi wannan tafiyan . SHIN SARKI HUMAIZ ZAI SAMU
NASARAR MALLAKAR KAMBUN TSAFI KUWA . WANI
IRIN MASIFU DA BALA'IEU ZAI HADA DASU . SHIN
BOKA KAMSUSULLAJANI ZAI AMINTA YAYI WANNAN
TAFIYA MAI MUGUN HADARIN KUWA . WANI UKUBA
NE SUkA AfKA ACIKI WANDA IN HAR BASU MALLAKI
WANNAN KAMBUN BA tOH ZASU HALLAKA . Domin jin
amsoshin wayannan tambayoyi Toh sai ku download na littafin anan
DOWNLOAD AS TXT/ DAUKO SHI A MATSAYIN TXT


DOWNLOAD AS PDF/ DAUKO SHI A MATSAYIN PDF

DOWNLOAD AS DOC/ DAUKO SHI A MATSAYIN DOC

0 Response to "NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 na Shuraih Usman"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel