TSATSUBA littafi na biyu 2

TSATSUBA littafi na biyu 2
Sunday, 12 August 2018


TSATSUBA

Littafi na biyu

Hausa ebooks

Abdulaziz Sani m Gini

Made by Shuraih Usman

Typing:- Al'amin Ahmed Misau



•••••••••••••••••••••••••••••••••
Kadan daga ciki
Part B.
.
Yayinda tsoho Imshal yaji wannan tambaya sai yayi
Ajiyar numfashi ya dubi sarauniya larbisa cikin
nutsuwa yace yake wannan sarauniya mai daraja
kiyi sani cewa ba wani abu bane ya sakikaga na bushe
da dariya ba sai saboda nasan cewa kin daukowa
kanki gagarumin aikin da sai kinyi nadamar yinsa
domin aikine wanda babu tabbacin samun nasara
a kansa, sannan kuma zaki iya shan bakar wahala
da bata da misali kuma dake da duk abikan
tafiyar taku zaku iya rasa rayuwarku ko lafiyarku.
Ke a takaice dai fiye da shekaru dari baya ba a
taba samun mahalukin da ya ratsa ta cikin wadannan
dazuzzuka guda uku har ya isa kogin sihir a raye
ba
don haka ni yanzu ina kallonki ne a matsayin wacce
ta gaji da rayuwar duniya take neman mutuwa ruwa
a jallo! Ko kuma ince wacce ta sami tabin hankali !!
Dalilin da yasa kikaga ina zubar da hawaye kuwa shine
biwa wannan TAFARKI da kike son bine na rasa
iyayena da kakannina domin suma sun bar gida
sun tafi izuwa kogon kitabul sihir domin magance wata matsala data addabi gaba
daya zuri armu tsawon shekaru masu yawa
amma dayansu bai dawo a raye ba, wannan matsala
kuwa ba komai bace face wani sihiri wanda wani abokin gabarmu ya yiwa kakanninmu, shi dai wannan abokin
gaba namu mafarauci ne kuma takadarin boka ne
tunda akayi GASAR FARAUTA a birninmu kakanmu ya lashe gasar sai wannan
boka yayi masa sihiri ya kasa ci gaba da zama a cikin
gari shi da iyalinsa yaji kamar ana konashi da wuta
Matansa da 'ya'yansa da jikokinsa ma haka suka rinkaji
ya zamana cewa ba shiri suka hada nasu 'i' nasu suka koma cikin daji da zama
bisa dole kakan namu ya hakura da sarautar sarkin
daji da aka bashi ya daina zuwa fada gaba dayan
zuri armu sai suka tsani cikin gari daga wannan rana kawo
iyanzu babu sauran mutum daya daga cikin zuri armu
wanda ke rayuwa a cikin daji duk mun watsu a cikin
dazuzzuka har yau har gobe ni din nan da matata da
yata shumaira da kike ganinmu bamu taba shiga cikin gari ba mu tsaya
tsawon rabin sa a sai dai muyi siyayya a kasuwa mu
fito babu irin kokarin da bamu yi ba wajan neman
yadda zamu karya wannan sihiri amma abu ya gagara
kafin mahaifina ya rasu ya shaida mini cewa ba
zamu taba iya samun nasarar karya wannan sihiri
ba face mun bude littafin TSATSUBA mun karanta wata kalmar tsafi guda
daya wadda ke shafin tsakiya , yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani
cewa bukatarki kusan iri daya ce da tamu amma ni ba zan
iya barin yata shumaira tayi wannan tafiya ba
tunda ita kadai gareni a wannan duniya kinga nidai tsufa ya riskeni mahaifiyar tama gata nan ta fara manyanta , yau idan babu ita shikenan zuri armu gaba daya ta shude kenan tunda
mu ne kadai mukayi saura
kafin tsoho Imshal ya gama rufe bakinsa sai jaruma shumaira ta mike zumbur ta durkusa bisa guiwoyinta a gabansa ta rike hannayansa biyu
a lokacin da hawaye ya zumo mata tace ya kai abbana kayi
sani cewa ko ka barni ko ka hanani yin wannan tafiya watarana sai mutuwa
ta daukeni
shin ka manta cewar ka gaya mini cewa dukkan mai nema
yana tare da samu lallai ina son na karya wannan asiri wanda ya gagari
iyayenmu da kakanninmu domin na barwa birninmu
abin tarihin da baza a taba mancewa dashi ba ka tuna cewa har yanzu sarautar
sarkin daji tana hannun zuri ar babban makiyinmu boka zarratu tunda mu mun kasa
zama a cikin gari
lallai ta kowanne hali saina kwato mana yancinmu na dawo mana
da sarautarmu mun koma mun zauna a cikin
wannan gidan sarauta namu na sarkin daji wanda
kai kanka rabonka da shi tun kana jariri ina mai rokonka daka bani wannan dama ayi
wannan tafiya dani
da izinin iyayenka dake kwance cikin kabari saina sami nasara
na kwato mana
yancinmu.
koda jaruma shumaira tazo nan a zancenta sai tsoho Imshal
da matarsa larisa suka kamu da tsananin tausayinta suka
rungumeta sunamasu fashewa da kuka itama
saita tayasu kukan
Al amarin da ya karya zuciyar sarauniya larbisa
kenan a karon farko a rayuwarta taji tausayin wani
ya kamata har itama idanunta suka ciko da kwalla kuma ba komai bane
ya janyo hakan ba face ganin matsalar ta tazo
iri daya da tasu
Saida tsoho Imshal da larisa suka dan jima a kankame
da shumaira sannan imshan ya janye jikinsa
daga cikin na shumaira ya
dubeta cikin Alamun tsananin damuwa yace yake
yata hakika kinzo mini da babban Al amari wanda ya dugunzuma hankalina kuma wanda a halin yanzu ba zan iya yanke
hukunci ba a kansa lallai ina bukatar ki bani lokaci daga nan zuwa gobe muyi
tunani da nazari akan al amarin nida mahaifiyarki
koda jin wannan batu sai hankalin sarauniya larbisa ya dugunzuma
ainun fiye da ko yaushe domin ta fara tunanin
cewa tsoho Imshal ba zai yarda da wannan tafiya
ba don haka duk shirinta ya rushe,
Nan dai shumaira ta mike tsaye ta kama hannun
sarauniya larbisa ta jata suka fice daga cikin falon
duk su biyun jikinsu a sanyaye, •••••••••••••••••••••••••••••••••

DOWNLOAD AS PDF EBOOK


DOWNLOAD AS DOC EBOOK



DOWNLOAD AS TXT EBOOK



Kar dai ku manta littafin kala Uku ne akwai TXT,PDF da DOC sai ku zabi wanda zai iya budewa a cikin wayoyinku batare da wata mishkila ba
.


Daga taskar hausaebooks
www.shuraih.waphall.com

0 Response to "TSATSUBA littafi na biyu 2"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel