GUDUN TSIRA littafi na Daya 1 na Abdulaziz Sani m gini
Saturday, 11 August 2018

GUDUN TSIRA 1 Hausaebooks
Download for free
Kadan daga ciki
Ko kifta ido
bayayi sai kace gunki.har Siyama da
dakarunta suka iso daf da karagar
mulkin tasa suka zube kasa gabansa
suka kwashi gaisuwa bai iya cewa
komai ba.Siyama ta mike tsaye ta
dago kanta sukayi arba ita da Sarki
Ruguzan a lokacin da da fuskarta ya
cika da annuri gami da murmushi mai
taushi tace ya kai wannan sarki mai
daraja gami da cikar mulki kayi sani
cewa mu kabilar Banu Hanzar mun
kasance talakawanka masu rauni da
kaskanci don haka mun zone neman
alfarama a wajenka bisa harajin da
muke biya a duk wata guda. Muna son
Sarki yayi mana adalci ya rage mana
kaso biyu daga cikin kaso ukun
abinda muke biya saboda tattalin
arzikinmu ya fara lalacewa.Koda
Siyama tazo nan a jawabinta sai Sarki
Ruguzan ya bushe da dariyar farin ciki
a lokacin da yaji wani irin girman kai
ya shigeshi.Lokaci guda kuma ya
hade fuskarsa ya dubi Siyama cikin
nutsuwa yace,yake wannan budurwa
ma'abociyar kyawu.Ke kuma wacece
a cikin mutanen Banu Hanzar kuma
me kuka zo mini dashi wanda zai sa
na amince da bukatarku?Siyama ta
dukar da kanta kasa tace Sunana
SIYAMA BIN SHARWAN 'ya ga
shugaban kabilar Banu Hanzar.Nazo
ne bisa wakilcin mahaifina.Ya
shugabana ba komai muka kawo
maka ba face Shanu da Tumaki guda
dari dari kacal don amfanin miyar
gidanka. Bamu da wani abu wanda
zamu iya baka amma muna neman
aldalcinka da jin kanka.Koda Sarki
Ruguzan yaji wannan batu sai ya bsue
da dariya a karo na biyu sannan ya
dubi wani babban hadiminsa yace
dashi a kai Siyama da jama'arta izuwa
masauki inda zasu huta kafin ya
zauna da 'yan majalisarsa su tattauna
dangane da bukatar datazo masa da
ita.Koda jin wannan batu sai hankalin
Siyama dana dakarunta ya tashi suka
fara tunanin cewa lallai akwai wani
abu wanda Sarki Ruguzan yake so
yayi na yaudara a garesu. Nan take
Siyama tayi dan guntun tunani sannan
ta dubi dakarun nata tayi musu inkiya
dasu kwantar da hankalinsu babu
abinda zai faru.Nan take aka tafi dasu
Siyama izuwa wani gida na
musamman inda ba a saukar kowa sai
manyan sarakuna da manyan
attajirai.Shi dai wannan gida an
kawata shi ainun ya cika aljannar
duniya babu abinda babu a cikinsa na
jin dadi.Da shigarsu suka iske an
kawo masu abinci na alfarma irin
wadanda ma basu taba ci ba sama da
kala ashirin an shirya shi akan tebur
sannan ga kayan shaye shaye ma iri
iri cikin tambulan- tambulan wanda
akayi shi daga 'ya'yan itatuwa nau'i
nau'i.Koda ganin wanna daula sai
dakarun Siyama suka dimauce basu
san sa'adda suka hau kan teburin ba
suka dasawa abincin wawa.Kawai sai
sukaji Siyama ta daka mus tsawa.
Cikin razana suka mike tsaitsaye
suka sunkui da kawunansu kas.A
sannan ne Siyama ta dubesu a fusace
tace shin a tunaninku Sarki Ruguzan
zai yi mana wannan kyau tane a
banza?Ku tuna cewa iyayenmu da
kakanninmu basu taba shigowa gidan
sarautar nan ba fiye da shekaru dari
da suka gabata.Basu taba dandanar
abinci mai dadi ba irin wannan kuma
sunyi zamaninsu tafiya sun tafi.Mu
hakura da irin yanayin rayuwarmu da
muka saba da ita kada a rudemu da
dadin duniya a cutar damu.Na lura da
wani irin kallo wanda Sarki Ruguzan
ya dinga yi mini,kallo ne na sha'awa
don haka idan harma zai biya mana
bukatarmu bada zuciya daya zai
taimakemu ba.Lokacin da Siyama tazo
nan a zancenta sai dakarun nata suka
shiga taitayinsu sosai.Babban cikinsu
wanda ake kira da Ilmar ya dubeta
yace,ya shugabata yanzu mene ne
abinyi kenan?Siyama ta numfasa tace
zamu jira daga nan zuwa yamma muji
irin shawarar da sarki Ruguzan yayi
da jama'arsa. Idan ban gamsu da ita
ba nasan abinda zanyi.Amma abinda
nake so daku shine dayanku ya zauna
a cikin shirin komawa can daji
sansaninmu nan da cikar dakiku
kadan bayan na gama rubuta wasikar
dazan bayar a kaiwa mahaifina.Koda
jin wannan batu sai su Ilmar suka cika
da tsananin mamaki kuma suka kasa
gane abinda Siyama ke kokarin
shiryawa.Har Ilmar ya budi baki zaiyi
mata tambaya sai ta daka masa
harara tace kada kuyi mini tambayar
komai kawai ku zamo masu bin
umarnina.Tana gama fadin hakan ta
bude jakarta ta fata ta fiddo alkalami
da tauwada gami da takarda ta koma
nesa kadan dasu Ilmar ta zauna ta
rubuta wasika. Bayan ta gama rubuta
wasikar sai ta nannadeta ta mikawa
daya daga cikin dakarun ya karba
sannan ta dubeshi tace Ya kai Muzaru
ka boye wannan wasikar a jikinka
yadda duk duban da za ayi baza a
ganta ba a lokacin da zaka fice daga
cikin garin nan.Lallai ka ruga izuwa
sansaninmu ka kaiwa mahaifina ita a
cikin kankanin lokaci kuma ka bashi
wannan wasikar a sirrance ba tare da
kowa ya sani ba.Koda jin wannan batu
sai Muzaru ya risina yace An
gama.Nan take Muzaru ya shiga cikin
bandaki ya kimtsa kansa sanna ya fito
da sauri yana fitowa sai Siyama ta
dubeshi tace duk wanda ya tuhumeka
dalilin tafiyarka yanzu ka gaya masa
cewar nice na aikeka wajen mahaifina
domin ka gaya nasa halin da ake ciki
don kar yaga mun dade bamu dawo
ba ya zata ba lafiya. Muzaru ya sake
risina yace An gama.Kawai sai ya
juya ya fice daga gidan gaba daya da
sauri.Kafin Muzaru ya fice daga cikin
gidan sarautar saida ya ratsa ta cikin
kofofi tara,kuma duk inda ya iso sai
an caje ko ina a jikinsa ba aga
wannan wasika ba da Siyama ta
bashi,kuma sai an tuhumeshi dalilin
dayasa ya fito shi kadai ba tare da
sauran abokan tafiyarsa ba,daya
basu amsar kamar yadda Siyama ta
umarceshi sai a bude masa kofar ya
wuce.Yana fita daga cikin gidan
sarautar ya zaburi dokinsa da gudun
tsiya ya nausa izuwa cikin daji,bai
tsaye a ko ina ba saida ya iso
sansaninsu inda suka kafa
tantuna.Tun daga nesa aka hango
Muzaru shi kadai ya dawo daga cikin
Birnin Kisra,sai hankalin kowa ya
dugunzuma aka fara tunanin ko wani
abu ya sami siyama da sauran
mukarrabanta.Koda isowar Muzaru
sai ya tsaida dokinsa a daidai kofar
tantin shugaba Sharwan ya
sauka,wani badakare ya kama dokin
nasa yaje ya daureshi. Nan take akayi
masa iso ya shiga cikin tantin.Da
shigarsa sai ya iske Sharwan tare da
mahaifiyar Siyama a zaune sunyi
jugum fuskokinsu a cike da alamomin
matukar damuwa da tashin
hankali.Koda ganin Muzaru sai
mahaifiyar Siyama ta mike zumbur ta
tareshi tana mai rike kafadunsa a
lokacin da idanuta suka ciko da kwalla
kamar zatayi kuka tace,ya kai Muzaru
ka gaya mini iyakar gaskiya,menene
ya faru ga 'yata?Muzaru yayi dan
guntun murmushi yace,Siyama tana
nan lafiya kalau kamar yadda kuka
ganni,yanzu haka itace ma ta bani
sako na kawowa shugaba,amma tace
sai na kadaita dashi.Koda jin wannan
batu sai shugaba Sharwan ya dubi
Matarsa Ilela cikin murmushi yace
barkanmu.Yanzu hankalinmu ya
kwanta.Yake matata bamu wuri na
gana da babban hadimi Muzaru.Ba
tare da gardamar komai ba kuwa Ilela
ta mike tsaye ta fice daga cikin
tantin.Fitarta ke da wuya sai Muzaru
ya kwance kitson kansa guda ya fiddo
wata takarda wadda take a kanannade
ya warwareta sannan ya mikawa
Sharwan cikin sauri kuma hannunsa
na karkarwa.Shugaba Sharwan ya
warware takardar ya karantata.Yana
gama karanta wasikar sai ya kurma
uban ihu ya durkushe kasa bisa
guiwoyinsa.Koda jin ihunsa sai
Mahaifiyar Siyama ta shigo cikin
tantin a firgice,ta rungumeshi sannan
ta fashe da kuka tanace yakai mijina
mene ya faru?Shugaba Sharwan ya
dubeta fuskarsa cike da damuwa
yace,yake matata kisani cewa damu
da dukkan 'yan kabilarmu muna cikin
babban tashin hakali. A wasikar ta
Siyama ta rubuto tace dukkanmu mu
hada inamu inamu mu bar wannan
daji mu kara gaba,sannan tace mu
hadu a wajen wannan katon dutsen,so
take mu bar wannan nahiyar gaba
daya.Bansan abinda take shirin
shiryawa ba,amma naji a jikina abin
ba dadi,in bamuy da gaske ba 'yan
kabilarmu guda daya bazata tsira da
ranta ba.Don haka yanzu mu fara
shirye shiryen barin wannan
waje.Koda jin wannan batu sai Ilela ta
sake kankame Sharwan tana mai
fashewa da matsanancin kuka. WANE
ABU SIYAMA TAKE SHIRIN AIKATA
WA? ME ZAI FARU A ZAMAN DA
SARKI RUGUZAN ZAIYI DA 'YAN
MAJALISARSA AKAN YANKE
WANNAN HUKUNCI? KABILAR SU
SIYAMA ZASUYI HIJIRA KO ZASU
ZAUNA,IDAN SUNYI HIJIRAR MAI ZAI
FARU DASU A GABA.
Domin jin cigaban wannan littafi sai ku download nashi anan
0 Response to "GUDUN TSIRA littafi na Daya 1 na Abdulaziz Sani m gini"
Post a Comment