ALLON SIHIRI na daya 1
Saturday, 11 August 2018

Kadan daga ciki
a fadin birnin Rauhul Bagadar babu mai yawan
shekarunta,domin shekarunta sun kai dari da
sittin,amma kuma Allah ya bata lafiya,idanunta garau
tana gani sosai,hakoranta duka suna nan reras daya bai
fadi
ba,kuma tana iya jure tafiyar yini guda ba
tare da gajiya ba.Tsohuwa Dulaiba tana da kaifin
basira gami da hangen nesa,don haka duk
sarakunan da akayi a birnin Rauhul Bagadar basu
da wani abokin shawara sama da ita,kuma bata taba
bayar da shawara akabi akayi nadama ba.Lokacin da
sarauniya Akisatul Sauwara ta kadaita da tsohuwa
Dulaiba a cikin turakarta sai ta kwashe labarin duk
abinda ya faru tsakaninta da Yarima Lubainu ta
zayyane mata,kuma ta nemi shawararta bisa abinda
ya kamata tayi.Koda jin wannan batu sai tsohuwa Dulaiba
ta
kyalkyale da dariya.Al'amarin dayai
mutukar baiwa Akisatul Sauwara namaki kenan ta
dubeta cikin mamaki tace,yake Dulaiba ina dalilin
wannan dariya taki?Koda Dulaiba taji wannan
tambaya sai ta nutsu tace,ki karbi wannan bako
hannu biyu,kiyi masa duk abinda yake so,domin a
sanadinsa
ne zamu cika burin da kakanninki suka
kasa cikawa tun kafin a haifeni ni kaina.Ki sani cewa
wannan barin Allon sihiri dake cikin gidan tarihin
garin nan wanda aka sanya shi a cikin kwalba ya
zamana cewa duk duniya ke kadaice zaki iya fito da
shi to duk ranar da aka samo ragowar barinka biyun aka
hadashi aka dora allon akan gunkin dake
tsakiyar fadarki sai Birninmu ya sami daukaka da
arzikin da babu wata kasa dazata kaishi kuma har
abada baza a cimu da yaki ba har sai mun mallake
gaba dayan kasashen duniya sun dawo karkashin
mulkinmu.Wannan shine burin da iyayenki da kakannink
suka
kasa cikawa amma yanzu ke kin
sami babbar dama ta cika wannan buri.Abinda zakiyi
shine ki dauko wannan Allon Sihiri amma kada ki
damkawa Yarima Lubainu a hannunsa.Ki boyeshi a
tare dake dare da rana kuma ki bishi kuyi wannan
tafiya tare har izuwa sauran kasashen biyu inda za'a sami
ragowar barikan Allon biyu.Da zarar an samo
su saiki shammaci Lubainu ki kwashe Allunan ki
bace.Na san cewa ke gagarumar jaruma ce kuma
mayakiya mai tarin sirrikan tsafi don haka ko gaba
da gaba zakiyi dashi sai kin sami nasarar
hallakashi.Idan ya tambayeki dalilin dayasa kike son ki
bishi
kuyi tafiyar tare kice dashi saboda a
rayuwarki babu abinda kike so sama da tafiya.Koda
tsohuwa Dulaiba tazo nan a zancenta sai Sarauniya
Akisatul Sauwara ta gamu da tsananin farin ciki
kuma ta sami nutsuwa gami da kwanciyar
hankali.
washe gari kuwa da safe sai sarauniya Akisatul Sauwara ta
tura
aka zo da Yarima Lubainu
har cikin turakarya in ya riske a kishingide bisa wata
doguwar kujera ta alfarma tana shan ruwan inibi a
cikin wani kofin zinare.A wannan lokacin tana sanye
da wata jar riga mai shara shara wacce take bayyana
dukkan surar jikinta.Koda Yarima Lubainu yayi arba da
Akisatul
Sauwara cikin wannan hali sai zuciyarsa
ta buga da karfi,yayi sauri ya sunkui da kansa
kas.Ba komai ne yasa shi hakan ba face gani yayi
kamar masoyiyarsa ce Yazarina zaune a wajen
saboda komai irin na surar jikin Akisatul Sauwara
yazo iri daya sak dana Yazarina tamkar Hassana da
Hussaina
suke.
Kawai a kamannin fuska ne suka
bambanta.Tabbas Sarauniya Akisatul Sauwara ta
cika kyakkyawar mace abin kwatance,To wai shin
mene ne abinda ya hana wannan kyakyawar
sarauniya yin aure alhalin tana cikin kuruciyarta don
baza takai shekara ashirin ba a duniya?Wannan itace
tambayar
da Yarima Lubainu ya yiwa kansa kuma ya
kasa bada amsarta.Lokacin da Sarauniya Akisatul
Sauwara taga Yarima Lubainu yayi saurin kawar da
idanunsa ga barin kallonta ya sunkui da kansa sai ta
kyalkyale da dariya sannan ta dago hannunta guda
tana mai yiwa gaba daya kuyangin dake dakin inkiya
dasu fita su basu wuri.Nan take kuyangin suka cika
umarni.
Fitarsu ke da wuya sai Akisatul Sauwara ta
dauki wata abaya irin tasu ta saraunta ta yafa a
jikinta,wato ta suturce tsiraicinta sannan ta dauko
tambula na ruwan inibi gami da wani kofin zinare tazo
daf da
inda Lubainu ke tsaye ta kusanceshi
ainun yadda har suna iya jin numfashin juna,sannan
ta zuba masa ruwan inibin a kofin ta mika masa.Ba
tare da tsoron komai ba Lubainu ya karbi kofin ya
kurba.A sannan ne ta kama hannunsa taja shi izuwa
kan waccan doguwar kujera suka zauna tare ta dubeshi
fuskarta cike da annuri da murmushi
tace,yakai wannan 'dan Sarki kayi sani cewa kai ne
da namiji na farko wanda ya taba shigowa har nan
cikin turakata yasha ruwan inibina,kuma har
hannuna mai daraja ya taba nasa.Ka sani cewa ba
komai ne yasa ka sami wannan matsayi ba face saboda
kazo
min da babban al'amari wanda na dade
ina jiransa a rayuwata.Kafin nayi maka wani
cikakken bayani ina son ka sanar dani sirrin da yasa
kazo kasata neman barin Allon Sihiri ni kuma nayi
maka alkawarin zan dauko maka Allon Sihirin dake
hannuna amma bisa sharadi guda biyu.Sharadi na farko
shine
tafiyar da zakayi tare dani za'a tafi har a
gama hada Allon Sihirin uku.Sharadi na biyu kuma
shine zan ajiye nawa allon a hannuna bazan baka ba
har sai bayan an samo ragowar barikan biyu.Nasan
zakayi mamaki bisa dalilin dayasa na kafa maka
wadannan sharuddai to ka sani ba wani dalili bane face
kawai
ni a rayuwata babu abinda nake so sama
da
yin tafiya domin naga abubuwan al'ajabi,kuma nayi
gami da mugayen dabbobi da tsuntsaye don na
gano iyakar jarumtaka da sadaukantaka ta.
Lokacin
da Akisatul Sauwara tazo nan a jawabinta sai Yarima
Lubainu
yayi shiru yana tunanin da
mamaki,kawai har izuwa tsawon yan dakiku,daga
can sai yayi ajiyar zuciya yace shike nan na amince
da wadannan sharudai naki.Nan take Yarima
Lubainu ya kwashe labarin rayuwarsa kaf ya zaiyane
mata ba tare da ya boye komai ba.Ai kuwa yana gama
bata
labarin jikinta yayi sanyi don har saida
idanunta suka ciko da kwallah.Nan take taji
zuciyarta ta kama wasi wasi akan cewar bai kamata
ta yaudari Yarima Lubainu ba ta gudu da Allon Sihiri
bayan sun hadashi.Zaifi kyau ta rakashi har izuwa
kogin Bahar Imfal in yaso bayan bukatarsa ta biya sai ta
dawo
gida da Allon Sihirin ta cika nata
burin.Wata zuciyar kuma sai tace da ita,idan kikayi
haka kinyi babban kuskure tunda baki da tabbacin
zaki iya wucewa lafiya kuma a raye ta cikin
wadannan mugayen dazuzzuka guda uku kafin a
isa kogin Bahar Imfal.Kawai sai Sarauniya Akisatul
Sauwara ta dago kai ta dubi Yarima Lubainu cikin
alamun tausayawa tace,ka kwantar da hankalinka
yakai Lubainu,hakika na tausaya maka mutuka bisa
kaddarar daka tsinci kanka a ciki,kuma nayi maka
alkawari cewar zan taimaka maka da raina da jikina da
dukiyata har izuwa lokacin da bukatarka zata
biya.Ina so ka gama dukkan shirye shiryenka a yau
din nan amma zan shiga nawa shirin kuma yanzu
zamuje dakin da wannan Allon Sihiri yake na
daukoshi in yaso gobe da sassafe a lokacin da alfijir
ya keto zamu bar garin nan mu durfafi BIRNIN KIMRAS
domin
mu gana da SARKI DARMASU mu
sanar dashi bukatarmu ta barin wannan Allon Sihiri
dake hannunsa.Kayi sani cewa bana tunanin cewa
Sarki Darmasu zai amince ya bamu wannan barin
Allo dake hannunsa domin yau shekara kusan
bakwai kenan muna yaki a tsakanin kasashenmu akan
mallakar
Allon Sihirin amma abun ya gagari
kowanne bangare.Idan har kaga ya amince da fito
da Allon Sihirin dake hannunsa saidai idan shima
yana da wata bukatar dabam.Babban abinda yake
bani tsoro shine kamar yadda nake da tsaro akan
nawa Allon Sihirin haka shima Sarki Darmasu yake da
tsaro
akan nasa,kuma bazamu iya rabashi da
Allon ba da karfin damtse kona yaki da tsafi.Sa'adda
Sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai
hankalin Yarima Lubainu ya dugunzuma ya rasa
abinda yake masa dadi,kawai sai ya dubi sarauniya
Akisatul Sauwara yace,nikam bani da wani zabi wanda
yafi na
jarrabata sa'ata kawai don haka babu
gudu babu ja da baya a cikin wannan tafiya.Koda jin
haka sai fuskar sarauniya Akisatul Sauwara ta
fadada
da murmushi tace biyoni muje.Tana gama fadin
hakan ta juya ta fice daga cikin turakar shi kuma saiya
bita da
sauri a baya.
SHIN YARIMA LUBAINU ZAI SAMI NASARAR SAMO
ABINDA YA FITO NEMA?
A WANNE HALI YARIMA MANGUL DA MAHAIFINSA
SUKE CIKI?
INA LABARIN MATAR YARIMA LUBAINU(YAZARINA) DA
MAHAIFINSA?
ME ZAI FARU TSAKANIN SARKI DARMASU NA
BIRNIN KIMRAS DASU SARAUNIYA AKISATUL
SAUWARA ITA DA YARIMA LUBAINU YAYIN DA SUKA
JE GARESHI DON KARBAR BARIN ALLON SIHIRIN
HANNUNSA?
SHIN ZAI AMINTA YA BASU WANNAN BARIN ALLON
SIHIRIN?
Download full ebook here
Dauko cikakken littafin anan don sanin ya zata kaya
0 Response to "ALLON SIHIRI na daya 1"
Post a Comment