TAKOBIN JINI littafi na uku 3 na Shuraih Usman
Saturday, 11 August 2018

Kadan daga ciki
. . Wannan tsuntsuwa tai kasa cikin
kankanin lokaci ta sauko izuwa doron kasa ,tana sauka
wannan jarumin mai kirar sadaukai ya diro daga
samansa . . Sannan yafara tattaki yana nufan wajen da
su sarauniya lasmin suke ita da hilal . Yana karisowa
yace dasu" yaku wayannan jarumai shin kuna
mamakin ganina ne awannan lokaci . Shin kuna
tunanin ku biyu kadai ne zakui wannan tafiya izuwa
neman TAKOBIN JINI . Toh kusani nima ina daya daga
cikinku . Lasmin ta dubeshi sannan tace dashi yakai
wannan jarumi ma'aboci lullube fuska shin wanene kai
kuma daga ina kake . . Koda jin haka sai wannan bakon
jarumin ya cire hular dake kansa . Aiko yana cirewa sai
dakarun dake tare da sarauniya lasmin . Suka zube bisa
gwuiwowinsu suna gaisuwa gareshi baccin sun idar sai
sarkin yaki kumru ya kariso izuwa gabansa yana mai
cewa" ya shugabana ka gafarceni bisa dadewa danayi
ban iso gareka ba" . . Nan take wannan jarumi yadaga
masa hannu sa'annan yadubi su hilal yace dasu " nine
sarki gulmanu mai mulkar birnin ashdamir" . .
Sarauniya lasmin ta dubeshi sannan tace dashi "amma
mai yasa baka jiramu mun iso izuwa birnin ka ba"
Gulmanu ya sauke ajiyar zuciya sannan yace da ita "
tabbas bokana ya nuna min duk abin dayake faruwa
daku tun daga lokacin da kika fito daga gida har iyanzu
da kike dab da shiga birnina ,koda naga kun hadu da
jarumin da zamu fita nema sai nayi shirin fita sa'annan
na fito don tarbeku . Sannan kusani yanzu bazamu mu
shiga birnina ba zamu tafine izuwa cikin wancan tanti
daga nan sai muyi shawarar daga inda zamu fara
neman wannan takobi Yafada yana mai kallon hilal .
Hilal yai murmushi sannan yace dasu daza ku yarda ku
karbi Addinin musulunci da nikuma sai na dauko
maku takobin jini da hannuna kuma batare da zoben
wuta ba. . Koda gulmanu yaji haka sai ya bushe da
dariya sannan yace mai kasani yakai wannan jarumi ba
zamu taba yarda mu amshi wannan Addini naka ba .
Kasani ba za mu taba watsi da Addinin iyaye da
kakanni ba . Sannan da kake maganar mu amshi
Addinikan toh izan mun amsa menene Amfanin
takobin jinin . Addininka ya haramta tsafi mukuma
baza mu taba watsi da tsafi ba . . Lasmin ta dubeshi
tace yanzu mene abun daya kamata muyi . Anan
gulmanu yai nuni da hannunsa izuwa wani gefe take
sai tanti ta bayyana . Dukkansu suka nufi wannan tanti
amma banda sauran dakaru . Juyowar da gulmanu
zaiyi sai yai arba da shaddadu yana mai murtuke fuska
yana binsu izuwa cikin wannan tanti. Nan yadaka masa
tsawa yace"kai daedai matsayinka wajen tantin nan
badae cikinsa ba . Shaddadu ko sauraransa baiyiba in
banda sakai dayayi da nufin ya kutsa cikin tantin aiko
yana kutso kan gulmanu yai tsalle ya kaftara masa
dundu abaya sannan yai nuni da hannunsa gareshi
take ya fara daskare wa tundaga kan yatsun hannunsa
koda shaddadu yaga yana daskarewa sai ya kurma
wata irin ihu . . A yayin dayake ihunne gaba dayan
jikinsa ya daskare yakoma tamkar wani mutum
mutumi.
Download the ebook here
0 Response to "TAKOBIN JINI littafi na uku 3 na Shuraih Usman"
Post a Comment