GUDUN TSIRA littafi na hudu 4
Saturday, 11 August 2018

GUDUN TSIRA 4?
Abdulaziz sani m gini
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
•••••••••••••••••••••••
Toh masu karatu gashi dai yau Allah yayi mun kawo maku littafin GUDUN TSIRA na hudu wanda Abdulaziz sani madakin gini ya rubuta ,
,
|
Wannan littafi dai yana kunshe ne da daukan fansa, Gudun Tsira, wanda sai dakyar ake Tsiran
.
Wasu kabila ne wadda ake kira da banu hanzar suna Rayuwarsu acikin Dajin birnin Kisra,
Alokacin da shi kuma sarkin Kisra yayi bincike acikin tsafinsa ya gano cewan muddin kabilar banu hanzar suka cigaba da zama adoron kasa toh wata ran sai sunzo sun kwace mai sarautarsa shi kuma Aduniya babu abin daya ke so sama da sarauta, hakan ce tasa ya tsanan ta ma banu hanzar kudin haraji ta yadda baza su iya biya ba.
.
Su kuwa kabilar banu hanzar koda suka ga ya tsananta masu wannan haraji sai suka yi gangami bisa jagorancin yar shugabansu mai suna SIyama suka je har birnin kisra don su nemi rangwame abisa wannan haraji,
.
Sarkin kisra mai suna RUGUZAN mayen mata ne koda su siyama suka je gareshi sai ya hada wata kullalliya, don ya samu ya sadu da siyama sannan ya kasheta,
.
Hakan shi ya janyo mugun gumurzu a tsakaninsu wadda har takai ga sarki ruguzan ya rasa rayuwarsa, sannan siyama ta gudu
.
.
Abinda su siyama basu sani ba shine sun kashe macijine basu sare kansa ba.
Sannan sun tsokalo tsuliyar dodone
.
.
Domin kuwa sarki ruguzan yana da danuwa wanda ake kira yarima darwarz .
Yarima darwarz yayan ruguzan ne kuma duk duniya babu wanda yake so sama da sarki ruguzan , hasalima shine za abashi sarauta amma saboda son dayake wa dan uwansa sai yabar masa wannan sarauta,
.
.
Darwaz mugun Azzalumine kuma gawurtaccen sadaukine , wadda aduk nahiyar babu wani sadauki da zai iya kaishi kas
.
Alokacin da darwaz ya samu labarin mutuwar dan uwansa yayi kuka sosai sannan ya dauki Alkawarin sai ya nemo gaba daya kabilar banu hanzar yayi masu kisan Gilla
.
.
Agefe daya kuma akwai Boka hurgas
Boka hurgas bokan birnin kisra ne wanda burinsa shine ya mallaki birnin kisra gaba dayanta hakan yasa ya runga munafuntar sarki darwaz batare da ya sani ba
$
.
Toh tambayar anan dai shine
S
.
.
SHIN KABILAR BANU HANZAR ZASU IYA TSEREWA SU SARKI DARWAZ?
.
.
SHIN SARKI DARWAZ ZAI CIMMA KABILAR BANU HANZAR?
.
.
IZAN YA CIMMUSU WANI IRIN BAKIN GUMURZU ZA'A TAFKA
.
SHIN WANE BAN GARE NE KUKE GANI ZASU SAMU NASARA
.
.
Kai kar dai kuce ina ta lasa maku zuma a baka
Ga kadan daga ciki
•••••••••••••••••••••••••••••••
bata wani lokaci ba sai Siyama taja wadannan
dakaru suka falfalwa da gudu izuwa cikin daji suna
yin wani irin gudu na ban al'ajbi tamkar giftawar
tauraruwa mai wutsiya,kafin kace wani abu tuni sun
kule uma sun bace a cikin duhun daren.Saida su
Siyama sukayi 'yar doguwar tafiya ta yan dakiku
masu yawa tana kan gaba sannan ta tsaya cak
suma
dakarun guda dari biyu sai sukayi cirko cirko a
bayanta.Siyama ta tsuguna kasa ta kara kunnenta a
kasa tayi sauraro dan kadan sannan ta mike tsaye
zumbur ta yafito dakarun su duka sukayi mata
kawanya,tayi musu radar wata magana.Nan take
dakarun sukayi wani sihiri su duka a lokaci
guda.Kawai sai kasa ta tsage suka shige cikinta
kuma kasar wajen ta koma ta hade kamar wani abu
bai taba faruwa ba a wajen.Itama Siyama ta shige
cikin kasar ta kule.Faruwar hakan keda wuya da
kimanin tsawon rabin sa'a saiga dakarun birnin
Darul Hunam su da yawa bisa dawakai dauke da
muggan makamai sun iso daidai wannan wuri.Da
isowarsu sai shugaban nasu ya daga hannu ya
tsaya.Take sauran yaran nasa ma suka ja linzamin
dawakansu,dawakan sukayi turjiya da
haniniya.Shugaban dakarun ya shaki kamshi har
sau
uku yace,tabbas zuga ta bil'adama ta tsaya a
nan.Kafin ya gama rufe bakinsa sai sukaji kasar
wajen ta kama tsagewa,dawakansu na ruftawa
ciki.Kafin dayansu yayi wani yunkuri duk an wurgo
musu wukake masu tsani sun caccake su a wuya
da
makogwaro.Nan fa suka rinka sulalewa kasa daga
kan dawakansu suna bajewa kasa matattu,kafin
kiftawar ido su duka sun zama gawa,sauran
shugabansu shi kadai a tsaye jikinsa na karkarwa
yana waige waige da dube dube,amma baiga
wanda
yayi musu wannan barna ba.Bazato ba tsammani
kuma sai yaga kasar ta kara tsagewa,sai ga dakaru
na fitowa sama daga cikin karkashin kasa su dari
biyu suna yi masa kawanya.Saida suka gama
fitowa
gaba dayansu sannan na cikon dari biyu da daya
ya
fito,kuma ba wani bane face Siyama.Kafafunta na
dira kan kasa saita durfafi shugaban wadannan
dakaru kai tsaye tana rike da sharbebiyar takobi,a
lokacin dashi kuma ya nutsu ya daina tsoron
komai
ya kura mata idanu kawai yana mai sadudar jin
kaifi
ya ratsa shi.Bisa mamaki sai yaji Siyama ta dora
fadin takobin akan kafadarsa sannan ta dubeshi
cikin
murmushin mugunta tace shin kana da iyali?
Mutumin yace kwarai kuwa inda da mace daya da
'ya daya.Siyama tayi murmushin murna tace nasan
zaka so ka koma garesu a raye,don bazasu so su
rasaka ba,kaima bazaka so ka rasa su ba.Idan
kabi
umarnina da dokokina zaka koma garesu a raye
kuma cikin koshin lafiya,amma fa idan ka sabawa
umarnina da dokokina ko
gawarka ma iyalin naka bazasu shaidata ba.A
yanzu
inason ka yi mama jagowa mu koma har izuwa
cikin
birninku kuma har cikin gidan sarautarku gaban
sarkinku a matsayin mune jama'arka ba a kashe
maka ko yaro daya ba,ka bar sauran yaranka ne a
baya.Kada ka kuskura kayi rawar baki ko ka
munafuncemu yadda asirinmu zai tonu.Idan kayi
haka tabbas a bakacin ranka.Koda gama fadin
hakan
sai Siyama ta dubi dakarun nata tayi musu
alama,nan take suka tube kayan matattun dakarun
suka sanya,kuma suka dau makamansu suke haye
kan dawakansu.Ita kuma Siyama sai tayi irin shiga
irin wannan,sannan tasa wannan shugaban
dakarun
ya hau nasa dokin itama ta hau dokin suka jera da
ita dashi.Sauran dakarun nata na biye dasu a
baya.Babu abinda zai baka mamaki a cikin wannan
hikima da Siyama tayi face yadda ta shirya
dakarun
nata girman jikinsu yazo iri daya dana dakarun da
suka kashe masu bin wannan shugaba a baya.Ita
kanta sai gashi jikinta yazo iri daya dana
mataimakinsa kai kace wancan din ne wanda aka
kashe
•••••••••••••••••••••••••••••
Yo ni dai ana zan tsaya domin jin yadda zata waka kuwa sai kuyi marmaza ku download na littafin zuwa kan wayoyinku ta hanyar danna wayannan blue din Rubutun
.
Kar dai ku manta :- littafin kala Uku ne akwai PDF,TXT da DOC sai ku zaba wanne manhaja kuke so kokuwa wanda zai iya budewa acikin wayoyinku ko kwamfitarku
.
.
Ga duk wanda yasan bai iya download na ebooks a shafina ba sai ya shiga nan yayi mani magana TA NAN
.
Sannan ina Gargadi
Ni bana Tura littafi a biyani sai dai inkaine da kanka kaga daman turomani da kudi don Allah
Bana saida Littafi a internet, domin sha'awa kadai nake hada ebooks don masu karatun hausa
.
Sannan bana whattsapp kuma bani da group a whattsapp
.
Kada wani ya ha'inceku ta hanyar amfani da Sunana a whattsapp
.
Gudun tsira 4 complet
Na Abdulaziz sani madakin gini
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so
For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521
Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum
Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) Abdulaziz sani m gini
Bissalam daga Shuraih Usman 99%
0 Response to "GUDUN TSIRA littafi na hudu 4"
Post a Comment