TA LEKO TA KOMA littafi na daya 1 dana biyu 2 a hade

TA LEKO TA KOMA littafi na daya 1 dana biyu 2 a hade
Saturday, 11 August 2018


TA LEKO TA KOMA 1&2

Na Nazir Adam Salih

Ebook creator:- Shuraih 99%

•••••••••••••••••••••••••••••••••


Kwamacalar chakwakiya,sauyin suburbuda, yanayin mazga da tsanTsar Zalunci



Assalam jama'a kaman ko yaushe yauma kuna tare dani ne Shuraih Usman inkiya 99%



Kaman kowanne sati yauma na shigo maku da wani kayataccen littafin Nazir Adam Salih wanda ya dade da bugashi



Shi dai wannan littafi yana kunshe ne da chakwakiya akan hodar iblis na kimanin Naira milya arba'in 40 million



Asalin hodar iblis din na wani Attajiri ne wanda ake kira da Alhaji banasare, inda ya dauki hodar iblis din ya baiwa wani yaronshi mai suna RAYYANU don ya fita mai dasu daga Nijeria,



Toh anan ne fa kwamacalar ta fara dun kuwa awani sashe dakwai SURAIYA MONIKA karuwa mai shirin Tuba, inda tayi kundunbala ta rutsa Rayyanu da bindiga ta kwaci hodar iblis din daga hannunsa hakan kuwa ya biyo bayan sakamakon kokarin kasheta da yayi ne



Asannan ne Alhaji banasare yaga TA LEKO TA KOMA don kuwa milyan arba'insa yabi Ruwa, alhaji banasare baiyarda da Rayyanu ba hakan tasa ya samu mataimakin kwamishinan yansanda AGANANI MUSHAGARA dan cin hanci da rashawa,
Ya bayyana masa duk Abin da ya faru



Shi kuwa mataimakin kwamishinan yansanda aganani mushagara irin mutanen ne masu hadama, nan da nan ya kulla ma alhaji banasare makirci aka kamashi, sannan yafara neman Suraiya monika dun ya karbi hodar iblis din



.
Acan gefe kuwa akwai wani matashin saurayi mai suna Haidar wanda shine silar duk faruwan wannan kwamacalar don kuwa da bai ci mutuncin Surayya monika ba da duk hakan bai faru ba



Kai karde na cika ku da surutu


¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤

Ga kadan daga cikin littafin

••••••••••••••••••••••••••••••••

Mahaukacin dukan kofar da ake yi shi ya farkar da
Surayya Monika daga cikin nannauyan barcin da take yi.
Da farko ta dauka mai gadinta ne Mu'azu,amma da ta
tuna da cewa ko wani abu muhimmi ne ya faru, mu'azu
ba ya buga mata kofa haka, sai dai ya danna kararrawa,
sanin haka shi ya sa Surayya
ta tashi a firgice. Cikin rudanin rashin sanin abin dake
faruwa. "Monika!" Taji wata kakkausar murya ta yi kiran
sunanta, sunan da aka fi sanin ta da shi a bariki. Ba ta
amsa kiran ba, ko da yake kafin ma ta amsa tuni an yi
mata zagi ya kai cikin kwando.
"Ki bude tun da ba gidan abanki ba ne" Aka ce da ita. "Na
ji Rayyanu ba gidan ubana ba ne. Ga ni nan kuma zan
bude tun da babu gadona a gidan"
Surayya ta amsa, a daidai lokacin ne ta matsa daga
bangaren arewa na falon in da tagar dakin take, sannan a
hankali ta janyo tagar ta leka, abin da ta gani ya sa ta
daukewar numfashi, ya kuma kafar da yawun bakinta. A
tsaye a bakin kofar dakin
Rayyanu ne tare da wasu samari majiya karfi guda
biyu, basu da kyan gani, dayan yana sanye da
doguwar riga fara jallabiya har kasa, kafarsa sanye cikin
takalmin roba, kansa babu hula, sai
nannadadden gashin da a ƙalla ya kai wata biyar bai ga
ruwa ba, hannunsa a cikin aljihun
jallabiyarsa, daya kuma hannun rike da bulalar
kebir. Saurayi na biyun shi ya fi ba ta tsoro,
fuskarsa irin wacce ka saba gani ce a duk lokacin daka
leka zagayen birirrika a gidan ajje naman daji (Zoo)
fuskar mai dauke da sharbeben bulle, da gashin baki irin
na kafiran da can, su suka sa hantar cikin Surayya kadawa
a take a nan taji gumi
ya rufe ta, ta san cewa yau za ta ga rashin mutunci.
.
An ya kuwa Rayyanu ne da kansa zai sa ayi mata Haka ba
taji tsoron bude kofar ba saboda tsabar tsoro da karaya
da ta yi kofar ta bude a hankali da farko, sannan daga
karshe ta taho da karfi ta hadu
da bangon dakin hakan shi ya sa wani bangaren
simunti daga jikin shafen dakin fadowa akan
sawun Surayya.
Surayya ta dubi Rayyanu, sannan shi ma ya dube ta,
tana sanye da duguwar riga ta barci, marar wadataccen
hannu. Kanta babu dankwali.
"marar mutunci nazo na ga iyakar rashin kunyarki"
"Ni ba marar kunya ba ce." Ta ce da shi.
Abin kamar hadin baki shimma Rayyanu yana daga
hannu sai ya talle ta da mari tas!!
"Ni ka mara Rayyanu?" ta ce da shi cikin shesshekar kuka,
"Sai ka gane kuskuren ka."
"Kuskurena?" Rayyanu ya ce yana dariya sannan
ya harari daya saurayin mai jallabiya.
Bai jira komai ba sai ya daga bulalar dake
hannunsa ya fara shararawa Surayya. Ta kwalla
kara mai tsanani a daidai lokacin da ruwan bulalar ya yi
ta zuba a gadon bayanta har sai da ta kasa
kuka abin kawai dake fitowa daga bakinta shi ne "Wayyo
Allah Haidar ka zo ka kwace ni dan kai fa ake yi min
wannan wulakancin! Wayyo Haidar ka
zo ka kwace ni kar ka bari na yi fushi da kai.." Tun tana
fadar haka har ta kasa. Bayan da Haji Rayyanu ya ga ta
kasa kuka sai ya
tsaida saurayin sannan ya kama hannun Surayya da
niyyar ya tashe ta, sai ta fadi kasa.
"Ku dauko min ita" Ya ce da samarin.
Mummunan ya kama kafafunta, shi kuma
mamuguncin ya kama hannunta suka yi mata cali- cali
suka nufi waje da ita. Haji Rayyanu ya bude but
din motarsa ya ce su jefa ta ciki suka jefa ta ciki,
sannan suka rufe. Mintuna biyu da yin haka sai can
mummunan nan ya nisa ya ce da Rayyanu "Ina jin
fa yarinyar nan ta mutu"
"Ni ma abin da na ke zato ke nan" Rayyanu ya ce. "Amma
abin da za mu yi shi ne mu kai ta can cikin
ciyayin nan na bakin kogi mu yarda ita da safe a tsince ta,
ni kuma daga nan zan sallame ku zan koma kwalambiya a
yau din nan. Daman babu wanda ya san na dawo, ko da
yansanda ko wasu
sun tsince ta babu wanda zai dora alhakin kisan kanta a
kaina tunda bana nan, kuma ku ma ku yi shiru da
bakinku."
.
"An gama Oga." Suka amsa baki daya. Bayan yan mintuna
suka isa bakin kogi karfe daya da rabi na dare babu kowa
a bakin kogin, suna zuwa suka bude bayan mota suka
sake yi mata cali-cali sannan suka zabi inda ya fi ko'ina
surkukiyar ciyayi suka jefa ta, ta faɗa amma ba ta motsa
ba, Rayyanu ya dube ta, sannan ya taka idon sawunta da
kafa
bata motsaba. Sannan suka shiga mota suka ware. Ba su
fi mintuna biyar da barin wajen ba aka tsinke da ruwan
sama kamar da bakin kwarya.
.
•••••••••••••••••••••••••••••••••

Hausawa sukace gani ya kori ji dun haka sai kuyi marmaza ku download na littafin zuwa kan wayoyinku ta hanyar danna wayannan blue din Rubutun
.





Kar dai ku manta :- littafin kala Uku ne akwai PDF,TXT da DOC sai ku zaba wanne manhaja kuke so kokuwa wanda zai iya budewa acikin wayoyinku ko kwamfitarku



.
Ga duk wanda yasan bai iya download na ebooks a shafina ba sai ya shiga nan yayi mani magana < a href="http://keffians.xtgem.com/forum">shafin tambaya

.


Sannan ina Gargadi



Ni bana Tura littafi a biyani sai dai inkaine da kanka kaga daman turomani da kudi don Allah
Bana saida Littafi a internet, domin sha'awa kadai nake hada ebooks don masu karatun hausa
.


Sannan bana whattsapp kuma bani da group a whattsapp
.


Kada wani ya ha'inceku ta hanyar amfani da Sunana a whattsapp
.


TALEKO TA KOMA complet
Na Nazir Adam Salih
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%



Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so




For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading



Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521 ko kuma 08173210359



Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu



Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya



Hakkin mallaka (m) nazir adam Salih






Bissalam daga Shuraih Usman 99%

0 Response to "TA LEKO TA KOMA littafi na daya 1 dana biyu 2 a hade"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel