SIRRINSU na Maje Elhajeej

SIRRINSU na Maje Elhajeej
Saturday, 11 August 2018


_ Shi kansa Nasir da maigadin
makabartar sunyi matukar fahimtar razana da
kidimewan dana yi.
Shakka babu na hadu da farida jiya a legos,kuma shakka
babu na bata zobena ,sannan shakka babu na tabbatar ta
mutu ,sannan shakka babu zoben dana tsinta akan
kabarin shine wanda na bata ta kuma saka ahannunta .
(Shakka babu nima shuraih wannan al'amri ya kidimani)
Shin yanzu wa zan gayawa wannan birkitaccen al'amari
ya gaskatani?
Wane ne zai yarda dani idan na ce jiya na hadu da mace a
Lagos ,kuma shekarunta uku da mutuwa ?"*_(shakka
babukoni bazan yadda dakaiba )_*
"Shine zoben daka bata" nasir yatambayeni cikin kaduwa.
"Shakka babu"cikin kidemewa na fadamasa.
"Nasir bana son kowa ya yarda da wannan rikirkitaccen
al'amari daya faru gareni,domin nasan shakka-babu babu
wanda zai gaskatani"
"Habib ! Ba na shakka,bana kokwanto wannan al'amari
daya faru zuciyata ta gaskatashi."
"Shin yanzu aljana ce ta fito min jiya a siffar farida?"*_
Shuraih Usman _*
"Shakka babu amsar kenan domin farida ta riga ta mutu"
***********
Sai da muka dawo kano na tuna ban tambayi nasir game
da kodaddiyar matar dana gansu da farida ba.
Shakka babu aljanu na hadu da su,domin kallo daya zaka
yi wa mummunar matar nan,ka san cewar aljana ce .
Natuna yadda na tsorata lokacin dana ganta ,da kuma
yadda naji na tsaneta .
Har muka dawo kano hoton farida da zobena da na bata ,
na kuma gan shi akan kabarinta ,
Sune abin da hankalina da tunanina suka tattara akai.
"Tunanin me kake yi habib?" Fatima fara mai matsa
kaicin tsayi da kauri,sanye da a tamfar Holland dinkin
sirfani,ta tambayeni tana murmushi.
"Tun dana kawo maka abnicin,har yanzu ko taba shiba
kayiba "
Nayi ga wurtacciyar ajiyar zuciya ,lokacin dana fito da
hoton farida daga aljihuna ,na kuma dora zoben
akai,sannan na mika mata .
*_ Shuraih Usman _*
Shakka babu kaki cin abinci kuma kamanninka sun
birkita ,wannan irin zukekiyar yarinya ,gaskiya kyakkyawa
ce "
Ta fada lokacin data dawo min da zoben, hoton har
yanzu na hannunta .
"So nake kikare ma zobennan kallo"
"Kamar ya nakare masa kallo,ba shine zoben dana baka
ba ?"Cikin mamki ta fada .
"Kin tabbatar shine "
"Shakka babu shine" Ta fada bayan ta kare masa kallo
sannan na kara zura shi a dan yatsana ,tun lokacin dana
daukeshi ban mayar dashi hannu na ba .
"Fatima ! So nake na yi maki wasu tambayoyi"
"Allah yasa ina da amsarsu"
Fatima ta kasance mace ma'abociyar ilmin Addinin
islama, ta bangaren tarihi,littatafan fiqhu,hadisai dakuma
Alqur ani.
"Shin ko a karance -karancen da kika yi na hadisai,dana
tarihi,da kuma na fiqhu zuwa Alqur'ani ,kokintaba karo
da cewar mutum idan ya mutu an binne shi,kan iya
tasowa yaci gaba da rayuwa?"




To kara kaka kara
Shin da gaske ne farida ta mutu ko kuwa tana raye
Dauko cikakken littafin akan wayanka tayadda zaka iya karantawa dakyau





0 Response to "SIRRINSU na Maje Elhajeej"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel