JARUMA YAZILA littafi na daya 1
Saturday, 11 August 2018

KADAN DAGA CIKI
daga wannan rana kowa
nuzaira tacigaba da renon jaririyarta da ranar suna
tazo sai aka radawa jaririya suna yazila tunda nuzaira
ta acikin wannan gida na mijinta acikin birnin kisra
batata bin hanyar gidan sarauta ba bare ma taga sarki
da idanunta bare kuma jairiyar datake raino. Tafiya
sannu sannu kwana nesa darare na wucewa kwanaki
na shudewa sai aka wayi gari yarinya yazila ta cika
shekara bakwai a duniya nan da yazila tazama
sananniya a birnin kisra saboda kasancewarta tataso
da tsananin kyau dakuma jarumantaka domin tun a
sannan tana iya daga kato komai girmansa ta
rankwalashi da kasa har sai datakai cewa ana shirya
mata gasar kokawa da mazaje majiya karfi tana zama
zakarar gasar daga nan kuma sai lamari nata kara
samun cigaba domin ta fara koyon sarrafa
takofi`mashi`kwarida baka. Duk mutumin daya fara
koya mata amfanida kayan yaki sai yaga tafi kwarewa
acikin kwanaki uku kacal. Tun da yazila ta taso taga
wata farar laya a wuyanta bata son abin da zai rabata
da layarba dare da rana har kwanciyar barci kuwa. A
takaice dai batata cire layarba kuma tana iya tuno
lokacin da mahaifiyarta hakimi barzuk ya samata layar
sa adda batafi shekara biyarba aduniya. Koda wasa
yazila batata bin hanyar gidan sarki ba kuma kojitayi
sarki zai shigo cikin gari tobazatataba fita daga cikin
gidan domin a rayuwarta babu data tsana tagani ko
taji zancensa face sarki. Abinda batasaniba shine.
Wannan laya da aka rataya mata awuya itace sanadin
dataji batason taga sarki.
Ana nan cikin wannan hali har yazila ta cika shekara
goma sha takwas. Alokacin ne kyawunta yaruda gaba
dayan jama ar birnin kisra ya zaman cewa duk inda
mutun yaje saidai yaji ana labarinta. Afagen jaruman
taka kuwa al amarin maya wuce tunanin mai tunani
domin duk sa adda aka fita yaki da mutanen birnin
misra tana ya musu mummunar barna wata jaruma
guda daya takeci mata tuwo akwarya wadda itace
sarkin yakin mutanen birnin misra a wani lokaci ita
dai larziya taji ana yiwa jarumar kirari da basadaukiya
dabira babban abin takaita awjen yazila shine
batataba ganin fuskar wannan abokiyar gaba tata ba
domin duk sa adda zata fito yaki tana rufe fuskarta ne
da hular karfe. Akalla yazila da dabira sun fafata
kazamin yaki kamar sau hudu amma duk sa adda suka
hadu.kare jini biri jini sukeyi. Koda rauni suka yiwa
juna sai kaga raunin yazo adadi daya baya gotawa
sukansu suna matukar mamakin wannan al amari
babu irin kokarin da yazila batayi ba don ganin ta cire
hular karfen datake dabira taga fuskarta amma abu ya
gagara.
Akwai.wata rana da dabira ta tambayi bokanta wanda
ake kira mushrid bin affan tace dashi yakai abin
dogarona yaza ayina sami nasara akan abokiyar gabata
absadaukiyar dabira na kai kasa kuma har na cire
hular karfen dake kanta naga fuskarta ?”
Koda jin wannan tambaya sai boka mushrid ya
kyalkyale da dariya sannan yace ” idan har kina son ki
sami wannan nasara sai dai ki cire wannan laya dake
wuyanki kije har cikin fadar sarki daksur ku yi arba da
juna in dai kikayi haka sai kin nasara akan jaruma
yazila har kiyi.mata rauni sama da adadin wanda
zatayi miki. Kuma ki kaita kasa ki cire hular karfen
dake kanta kiga fuskarta amma ki sani cewa ranar da
wannan tashin hankali irin wanda baki tabaga
shigarsab”
Koda jin wannan babu sai jaruma yazila tasa hannunta
ta kama wannan farar laya dake wuyanta da nufin ta
cireta amma sai ta ji kamar an soka mata allura guda
dubu a sassan jikinta. Ba shiri ta saki layar ta kama
ihu kuma ta fadi kasa a matukar galabaice tana haki
wadda aka yi yunkuri zare ruhinta. Nan ta jike sharkaf
da gumi da kyar ta dago da kanta ta dabi boka
mushrid tace ” meya sana kasa cire wannan laya daga
wuyana kuma taya ya zan iya rabuwa da ita ?”
*WACCE AMSA BOKA MUSHRID ZAI BAIWA JARUMA
YAZILA?
*YAUSHENE JARUMA YAZILA ZATA YI ARBA DA
FUSKAR SARKI DAKSUR?
*YAYA AKAYI BASADAUKIYA DABIRA TAZAMO SARKIN
YAKIN BIRNIN MISRA?
SHIN ITAMA TA ZAMA MUSULMA CE?
*I NA LABARIN MAHAIFIYARTA HUMAIRA?
*SHIN NUZAIRA DA HUMAIRA ZASU SAKE GANIN
JUNA?
Domin jin wayannan Amsoshi sai ku Download na littafin anan kasa
.
Zabi wadda kuke so
0 Response to "JARUMA YAZILA littafi na daya 1"
Post a Comment