ZAYYANA 1 & 2 na Nazir Adam Salih

ZAYYANA 1 & 2 na Nazir Adam Salih
Saturday, 11 August 2018


KADAN DAGA CIKI

Farida tayi ajiyar zuciya a tsorace sa'ar data fahimci cewa
idan ba wani ikon Allah ba itama kwanan nan aljanin zai
fara bugeta tuni ta fara nadamar zuwa gidan dan daudun
nan domin yi mata zanen kunshi akan tsaraicinta farida
ta riga tasan wannan kunshi shine sanadiyyar wannan
bala'in dake faruwa akanta daman mahaifiyarta tasha
fada mata cewa yawan fito da tsaraici a fili na cikin
abinda ke sa aljanu su hau kan mata.
Farida ta dubi tafin hannayenta dakuma bayansu batayi
mamaki ba sa'ar dataga zanen kunshin yadawo
rangadadau kamar ma yanzu aka zana shi duk kuwa da
cewa ta tabbata har lokacin da baba Ali ya sauketa
hannunta babu zanen kunshin.
Farida tayi matukar kyau awannan yammaci ita kanta ta
sani domin inka dauke yan littattafan dake hannunta duk
abin dake jikinta sabo ne tun daga kan riga da siket din da
mahaifiyarta ta sayo mata a landan zuwa ga takalmin
dake kafarta da yan kunnayenta da sarkoki kai hatta
alkalamin rubutun dake hannunta sabo ne domin dazun
ta saye shi. In banda farida ta riga tasan zanen kunshin
dake hannunta na aljanu ne da sai tace shima ya taimaka
wajen fito da kyawunta a fili.
Kai gaskiya yau kinyi bala'in haduwa.
Kabir yace sa'ar da farida ta karaso inda yake lokaci guda
kuma ya rage sautin kidan dake tashi.
Nagode farida tace a tausashe.
Naji dadi da kwalliyata tayi maka kyau Ah gaskiya tayimin
zagayo ki shigo ciki kabir yace sannan ya mika hannunsa
ya bude mata daya kofar.
Ahankali farida ta shigo cikin motar ta zauna sannan ta
rufo kofar, shima kabir ya rufe kofar ya kunna na'urar
sanyi kana ya dubeta farida ta lura da irin kallon dayakeyi
mata dan haka cikin bin umarnin shaidaniyar kawarta
Asma'u saita dan bude gaban rigarta kadan domin kabir
ya sami damar hango tsakanin kirjinta sannan saita dan
matsa kusa da jikinsa ta dora kanta akan kafadarsa.
Ilove You Kabir.
Kabir yaji kamar ta watsa masa ruwan sanyi azuciya a
wannan dan takin dakikar saiyaji kaunarta ta mamaye
zuciyarsa amma a iya lokacin nan kawai kafin shaidan ya
maye gurbin da sha'awa.
Daga nan idan mun tashi ina zamu?
Kabir ya tambayeta yana wani lumlumshe idanu sannan
ya kama hannayenta biyu yana kallon zanen kunshin
dake jiki.
Farida ta dubeshi cikin mamaki tace
Gida mana ba gida kace zaka kaini ba?
Kabir ya dubeta ido da ido ya girgiza kai yace, sai mun
fara biyawa ta gidan wani abokina kafin nakai ki gidan
domin can zamufi samun sake.
Farida taji gabanta ya fadi bata dauka abin zaikai ga haka
ba yaushe za'ace ta bishi wani gidan aboki.
Ina ganin muyi hirarmu anan dai zaifi kyau... Farida tace
a tausashe zuciyarta na harbawa tana tsoron kada ta
batawa kabir rai.
Kabir ya kamo tafukan hannayenta guda biyu ya dorasu
akan fuskarsa yace.
Ina kaunar ki ne farida shi yasa na nemi ki bini domin in
nuna miki yadda nake kaunarki.
Farida taji gabanta ya fadi ahankali ta zame hannayenta a
wayance daga kan fuskarsa.
Haba farida bakya.... Kalmar ta makale a fatar bakin kabir
sa'ar dayaga yanayin fuskar farida ta sauya nan da nan da
kabir ya kalli fuskarsa a jikin madubi alokacin daya hangi
irin zanen kunshin dake tafin hannunta rangadadau a
zane akan kumatunsa kamar yi masa akayi.
Kada ki damu idan bakya son zuwa yanzu maje watarana
kabir yace da ita cikin sauri shi a haukansa ya dauka
abinda yace ne ya birkita kamanninta.
Farida ta gyada kai babu magana idanunta zuru akan
zanen fulawar dake kan kumatunsa.
Ganin haryanzu batayi fara'a ba sai kabir ya rankwafa
jikinta yana cewa haba farida....kiyi min murmushi mana
konaji dan dadi dadi yana gama fadin haka sai ya zura
hannayensa ya tallafo kanta sannan ya tura bakinsa gaba
da nufin zai sumbaceta anan ne to wani abu mai kamar
hannu ya zuro cikin motar kamar daga sama ya kifawa
Kabir Mari.
Wayyo Allah... Kabir yasa ihu sa'ar da yaga wani haske
kamar wuta ya gifta akan fuskarsa.
Wayyo... Wayyo dan Allah ki taimakeni za'a kasheni kabir
ya sake kwala ihu sannan a rude sai ya bude kofar motar
ya fada kasa yana birgima afilin ajje motoci na jami'ar
bayero.
Daga yau ka sake lalata ya'yan mutane dan banza
lalatacce an fadama matata irin matan da zaka iya tabawa
ce.
Wata kakkausar murya tace daga sama sannan sai aka
kece da kakkausar dariya.
Tsananin kaduwa da tsoro su suka hana farida yin motsi
tana nan zaune akan kujerar motar kamar gunki tana
hangen kabir yana ta murkususu adaidai lokacin ne to ta
lura da wasu fararen abubuwa masu kama da kashi akan
cinyarta hannunta na rawa farida ta dauki fafaren
abubuwan. Saida ta kura musu idanu sannan ta gane
ashe Hakoran mutum ne guda uku wannan shiya sata
bude kofar motar ta fice aguje sannan tasa kabir agaba ta
fara Ihu.
Nan da nan gurin ya cika da dalibai hadiman jami'ar
masu gadi da shara aka zagaye kabir an rasa mai taba shi
can sai wani kakkarfan dattijo mai shara ya matso ya
tashi kabir da kyar daga kan fuskarsa jini na zuba nan da
nan daliban dake zagaye dashi suka rike numfashi a
razane sa'ar da sukaga bakin Kabir ya karkace ya koma
baya gashi babu hakoran gaba.
Ku kamamin mu shiga dashi cikin makaranta ayi masa
addu'a ina zaton aljanu ne suka shafe shi. Dattijon yace.

.

Wai shin wanene wannan daya mari kabir


Shin akwai aljanin da gaske


Ta yaya akayi har aljani ya shiga jikin farida


Domin jin wayannan amsoshi
Sai ku downloading wannan littafi anan







0 Response to "ZAYYANA 1 & 2 na Nazir Adam Salih"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel